Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince tare da bayar da umarnin gaggawa na rushe duk wasu gine-gine da aka yi akan magudanun ruwan kwarin Gogau da ta haddasa ambaliyar ruwa a Kano.
Haka kuma an tabbatar da binciko tare da rushe duk wani gini da aka yi a kan magudanun ruwan da suka zagaye kasuwar Kantin Kwari dominn bai wa ruwa damar kwaranyewa a yankin.
- Dambu Ya Yi Ajalin Mutane 7 ‘Yan Gida Daya A Sakkwato
- Yadda Bidiyon Tsiraicina Ya Karade Shafukan Sada Zumunta – Safara’u
Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labaran Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwar da aka gudanar a dakin taron fadar gwamnatin Kano.
Da yake karbar rahoton kwamitin gaggawa kan ambaliyar ruwan kasuwar Kantin Kwari wanda Kwamishinan, Ma’aikatar Ayyuka da Tsare-Tsare, Injiniya Idris Wada Saleh, da na Ma’aikatar Muhalli, Dakta Kabiru Ibrahim Getso, zaman majalisar zartarwar ya ba da umarnin rushe duk wasu gine gine-ginen wucin gadi da aka yi a zagayen kasuwar da cikinta nan ta ke.
Haka kuma, majalisar zartarwar ta kuma zartar da cewa a gaggauta kawar da duk wasu abubuwan da ke toshe magudanun ruwa da ke cikin kasuwar da zagayenta, tare da dauke duk wasu kayan gine-gine da aka ajiye a kan magudanun ruwan da ke cikin kasuwar.