An shiga tashin hankali a Masana’antar Ƙera Makaman Yaƙi ta Nijeriya (DICON) da ke cikin garin Kaduna lokacin da wani abun fashewa ya tarwatse.
Wakilinmu da Kai ziyara wurin da lamarin ya faru ya ruwairk cewa abin fashewar, wanda aka fara zaton bom ne da farko ya hallaka ma’aikata biyu a masana’antar yau Asabar, 20 ga watan Satumba, 2027.
Wannan lamari dai ya tada hankalan mutanen a kewayen masana’antar, wacce ke unguwar Kurmin Gwari a cikin birnin Kaduna.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu.
“Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana’anta ne,” inji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa.
Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp