Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Haruna Musa, ya yi kira ga ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da masu hannu da shuni a duk faɗin Nijeriya da su yi koyi da shirin karfafa ilimi na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Farfesa Musa, ya yi wannan kiran ne a kwanan baya a wajen bikin bayar da tallafin karatu a jami’ar da ke Kano, inda Sanata Jibrin ya bayar da takardar shaida ga wadanda suka ci gajiyar shirin su 1,000 daga mazaɓun sanatocin Kano ta Kudu da Kano ta Tsakiya don yin karatu a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina.
- Yawan Kudin Da Aka Kashe Na Zamantakewa A Watan Agusta A Kasar Sin Ya Kai RMB Triliyan 3.97
- Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Musa ya bayyana matakin a matsayin wanda zai taimaka matuƙa wajen ƙarfafawa matasa ilimi, yana mai jaddada cewa, “babu wani tallafi da ya wuce ilimi wanda kuma ake buƙata domin samun ci gaba”.
Mataimakin shugaban jami’ar ya ja hankalin gwamnati da cewa, yawan al’ummar Nijeriya kusan miliyan 230, kusan kashi 30 cikin 100 na matasa ne a halin yanzu ke makaranta ko kuma suke koyon sana’o’i.
Don haka, ya yi gargadin cewa, hakan ya bar wani kaso mai tsoka na matasa da ba su zuwa makaranta ko ba su da aikin yi, – lamarin da ya bayyana a matsayin “abin takaici da haɗari ga al’ummarmu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp