Wani sabon rikici ya kunno kai a Jihar Ribas bayan da majalisar dokokin jihar ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan yadda tsohon kantoman riƙon jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya tafiyar da kuɗaɗen jihar cikin watanni shida da ya yi a kan mulki.
‘Yan majalisar sun ce haƙƙinsu ne su binciki yadda aka kashe kuɗaɗen jama’a, duk da cewa Ibas ya ce ba huruminsu ba ne saboda shugaban ƙasa ne ya naɗa shi lokacin dokar ta-ɓaci.
- He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
- Jadawalin ‘Yan Wasa 30 Na Farko A Kyautar Ballon D’or Ta Bana
Ana zargin Ibas da almubazzaranci da kuma ƙin bin umarnin kotu, musamman kan naɗin shugabannin ƙananan hukumomi 23 na riƙo.
Ƙungiyoyi daga yankin Neja Delta ma sun buƙaci a bincike shi bisa zargin amfani da iko da kuma karkatar da kuɗaɗen jama’a.
Wasu ‘yan jihar sun yi maraba da wannan mataki suna cewa dama suna jira a binciki yadda aka kashe kusan Naira biliyan 250 da jihar ta samu a lokacin.
Sun ce manyan ayyuka sun tsaya cak a jihar, ma’aikata ma ba su samu albashin watan Agusta ba sai da gwamna Fubara ya bayar da umarni.
Sai dai Ibas ya yi watsi da wannan bincike, inda ya ce aikin banza ne kuma majalisar ba ta da ikon bincikensa.
Masana harkokin siyasa na ganin binciken na iya sake tayar da hayaniya a siyasar Ribas, musamman bayan ƙarewar wa’adin dokar ta-ɓaci a ranar 17 ga watan Satumba, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp