ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar

by Sadiq
1 year ago
Kano

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), ta tabbatar da ɓullar cutar Mpox a jihar.

Hukumar ta ce marasa lafiyar da suka kamu da cutar sun warke gaba ɗaya kuma an sallame su.

  • He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
  • Jadawalin ‘Yan Wasa 30 Na Farko A Kyautar Ballon D’or Ta Bana

Daraktan KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu Abbas ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce mutum biyun sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Birni da Ungogo.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa duk mutanen da suka yi hulɗa da marasa lafiyar an yi musu gwaji, kuma babu wanda aka samu da cutar.

Farfesa Abbas ya bayyana cewa wannan tabbaci ya biyo bayan gargaɗin da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta yi, na kiran jihohi da su ƙara sa ido kan ɓarkewar cututtuka kamar COVID-19, Ebola, Zazzaɓin Lassa, Marburg da Mpox.

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Ceto Rarara Yayin Da Wasu Fusatattun Matasa Suka Yi Yunƙurin Lakaɗa Masa Duka A Abuja

ASUU Ta Fara Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara Kan Rashin Biyan Albashi

Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.

KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.

Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.

Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.

Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.

Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Ceto Rarara Yayin Da Wasu Fusatattun Matasa Suka Yi Yunƙurin Lakaɗa Masa Duka A Abuja
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Ceto Rarara Yayin Da Wasu Fusatattun Matasa Suka Yi Yunƙurin Lakaɗa Masa Duka A Abuja

November 21, 2026
ASUU Ta Fara Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara Kan Rashin Biyan Albashi
Manyan Labarai

ASUU Ta Fara Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara Kan Rashin Biyan Albashi

November 20, 2026
2027: Makinde Ya Yi Alkawarin Sauya Tsarin Mallakar Albarkatun Kasa A Nijeriya
Manyan Labarai

2027: Makinde Ya Yi Alkawarin Sauya Tsarin Mallakar Albarkatun Kasa A Nijeriya

November 20, 2026
Next Post
Rikicin Gonar Gado Ya Yi Ajalin Mutum Ɗaya, An Ƙone Gidaje A Filato

'Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Ceto Rarara Yayin Da Wasu Fusatattun Matasa Suka Yi Yunƙurin Lakaɗa Masa Duka A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Ceto Rarara Yayin Da Wasu Fusatattun Matasa Suka Yi Yunƙurin Lakaɗa Masa Duka A Abuja

November 21, 2026
ASUU Ta Fara Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara Kan Rashin Biyan Albashi

ASUU Ta Fara Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara Kan Rashin Biyan Albashi

November 20, 2026
Kamfanin MAGGI Ya Raba Motoci Da Miliyoyin Kuɗaɗe Ga Abokan Hulɗa A Bikin Cika Shekara 60 A Nijeriya

Kamfanin MAGGI Ya Raba Motoci Da Miliyoyin Kuɗaɗe Ga Abokan Hulɗa A Bikin Cika Shekara 60 A Nijeriya

November 20, 2026
Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ta Asiya Da Tekun Fasifik: Wani Sabon Tsari Mai Habaka Hadin Gwiwa A Yankin

Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ta Asiya Da Tekun Fasifik: Wani Sabon Tsari Mai Habaka Hadin Gwiwa A Yankin

November 20, 2026
Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ta Asiya Da Tekun Fasifk Ta Shiga Sabon Mataki Mai Inganci

Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ta Asiya Da Tekun Fasifk Ta Shiga Sabon Mataki Mai Inganci

November 20, 2026
An Kai Wa Tsohon Kyaftin Ɗin Super Eagles, Segun Odegbami, Hari A Gidansa Da Ke Ogun

An Kai Wa Tsohon Kyaftin Ɗin Super Eagles, Segun Odegbami, Hari A Gidansa Da Ke Ogun

November 20, 2026
2027: Makinde Ya Yi Alkawarin Sauya Tsarin Mallakar Albarkatun Kasa A Nijeriya

2027: Makinde Ya Yi Alkawarin Sauya Tsarin Mallakar Albarkatun Kasa A Nijeriya

November 20, 2026
Dole Ƴan Crypto Da Forex Su Yi Rijistar Biyan Haraji Nan Da 30 Ga Nuwamba – NRS

Dole Ƴan Crypto Da Forex Su Yi Rijistar Biyan Haraji Nan Da 30 Ga Nuwamba – NRS

November 20, 2026
Jam’iyyun Adawa Sun Amince Su Dakatar Da Kamfe Don Tattaunawar Haɗin Kai

Jam’iyyun Adawa Sun Amince Su Dakatar Da Kamfe Don Tattaunawar Haɗin Kai

November 20, 2026
Wannan Ganawa Za Ta Taimakawa Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya

Wannan Ganawa Za Ta Taimakawa Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya

November 20, 2026

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.