Kungiyar Malaman jami’a(ASUU) ta sake ba gwamnati wasu sabbin sharuda kafin ta janye yajin aikin da take yi a halin yanzu.
Shugabankungiyar na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke,ya bayyana haka a zantawarsa da gidan talabijin na Channel, wanda kuma ya ce, dole sai gwamnati ta tabbatar musu da adalci kafin su koma bakin aiki.
“Gwamnati, ta gaya mana, ina aka saka makudan kudin da aka ware don bunkasa ilimi? Nawa ne kudin, kuma suna ina? Yaushe za a fito da su?” in ji Osodeke.Osodeke ya kara da cewa,dole gwamnati ta yi cikakken bayanin matsayinta a kan yadda za a warware matsalar UTAS, da tsarin biya ASUU da tsarin biya ta IPPIS.
“Bayan mun kulla yarjejeniya da su, sai suka kasa cika alkawari, kullum sai su fito suna gaya mana, mu kara hakuri,” In ji Osodeke.
“Yajin aiki alama ce da ke nuna cewa, akwai matsala. Duk lokacin da aka warware wannan matsala, babu kuma sauran yajin aiki.”
Inza a iya tuna wa dai, ASUU ta fara yajin aiki tun ranar 14, ga watan Fabrairu, 2022.