‘Yansanda a Jihar Ribas sun kama tsohon ɗan wasan Super Eagles, Victor Ezeji, kan zargin zambar kuɗi da suka kai Naira 39.8 miliyan da kuma barazana ga rayuwar wani.
Rundunar ta ce Ezeji da matarsa sun sayi lita 60,000 ta dizal daga wani ɗan kasuwa, Dagogo Emmanuel, amma takardun biyan kuɗin da suka bayar ba su cika ba.
- Majalisar Dattawa Ta Buɗe Ofishin Sanata Natasha
- Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa
An ce ma’auratan sun ɓuya tun daga watan Yuli kafin daga baya a kama Ezeji a Fatakwal ranar 22 ga watan Satumba, 2025.
Ya amince da sanya hannu a takardun kuɗin amma ya ce matarsa ce ta yi hulɗar kasuwancin gaba ɗaya, kuma bai san inda take ba.
‘Yansanda na cibgaba da neman ta.
Da6n uwansa, Chuks, ya tabbatar da kama shi, amma ya ce Victor ba shi da laifi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp