• English
  • Business News
Friday, September 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yancin Kananan Hukumomi: Yadda Gwamnoni Suke Kawo Cikas

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
5 hours ago
in Manyan Labarai
0
‘Yancin Kananan Hukumomi: Yadda Gwamnoni Suke Kawo Cikas
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Rashin baiwa Kananan Hukumomi ‘yancin gashin kai duk da hukuncin da Kotun Koli ta zartas sama da shekara daya na kawo karshen asusun hadin guiwa da wajibcin baiwa kananan hukumomi kudaden su kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya na ci-gaba da zama kalubale ga Kananan Hukumomi da koma baya ga mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.

A sassa da dama na kasar nan daga Tambuwal a Sakkwato zuwa Karaye a Kano, daga Ibarapa a Oyo zuwa Kachia a Kaduna al’amarin koma baya a kananan hukumomi ya zama tamkar inda babu gwamnati.

  • Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
  • Salon Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin: Hanya Ce Mallakar Kasar Sin Wacce Kuma Ta Sada Duniya

A kan wannan, muhawara kan ’yancin kananan hukumomi ta jima ta na daukar hankalin al’umma a Nijeriya musamman yadda Gwamnoni ke juya biliyoyin kudaden da ya kamata a yi wa al’umma ayyukan raya karkara.

A kokarin ganin gwamnoni sun bi umurnin kotun koli wadda ta zartas da hukuncin a watan Yuli 2024, Shugaban Kasa, Bola Tinubu a watan Satumba 2024 ya kafa kwamitin mutane 10 a karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da fara aiwatar da ‘yancin kananan hukumomi, sai dai sama da shekara daya babu abin da ya tabbata.

Kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ya bayyana kananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnati, tare da baiwa jihohi ikon gudanar da kudaden kananan ta asusun hadin guiwa, kudaden da gwamnoni ke rarbawa a zabin son ran su.

Labarai Masu Nasaba

NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba

Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa

A watan Yuli 2025, Kotun Koli ta zartas da hukuncin cewar dukkanin kudaden kananan hukumomi wajibi ne a tura su zuwa asusun su kai tsaye. Hukuncin hujja ce a dokan ce da ke kare ikon kananan hukumomi.

Sai dai gwamnoni sun ki bin umurnin ta hanyar ci-gaba da rike kudaden tare da juya su yadda suke so a biranen jihohi ba tare da raya karkara ba.

Da farko Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci Ministan Kudi da Akawun gwamnatin tarayya da su tabbatar da fara biyan kananan hukumomi kudaden su kai tsaye daga watan Satumba 2024, sai dai murna da fatar al’ummar karkara ta fara ganin sauyi ta koma ciki a yayin da har bayan shekara daya da hukuncin kotun koli da kuma umurnin shugaba Tinubu ba su gani a kasa ba.

A kalilan kudaden da gwamnoni ke ba su, rahotanni sun nuna cewa fiye da kashi 70% na ayyukan kananan hukumomi gwamnoni ne ke da wuka da naman fayyace ayyukan da za a aiwatar.

A kan wannan tuni majalisar kasa ta bayyana cewar za ta yi wa kundin tsarin mulki kasa gyaran fuska domin baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kai ta hanyar roshe asusun hadin guiwa.

Kananan Hukumomi suna karbar daruruwan miliyoyin kudade a kowane wata, hasalima babu karamar hukumar da ke karbar kasa da naira miliyan 300 a wata amma kuma ba su shiga hannun su ballantana su yi wa jama’ar karkara ayyuka.

Misali a watan Yuli 2025, kananan hukumomi 774 sun karbi tsabar kudi naira bilyan 485. 039 daga asusun gwamnatin tarayya. A watan Agusta 2025 kuwa, an rabawa kananan hukumomi naira bilyan 267. 652 amma kuma sam al’ummar karkara ba su ganin kudaden a ayyukan bunkasa yankunan.

A yau kananan hukumomi na ci-gaba da zama a mace a tabarbare saboda rashin ayyukan raya karkara da ci gaban al’umma da shugabannin yankunan ke kasa yi saboda takunkumin asusun hadin guiwa da ya dabaibaye su.

Al’ummar yankunan karkara sun dauki tsayin lokaci suna kuka da kokawa da rashin abubuwan more rayuwa wadanda sai dai su gani a biranen jihohi. Masana sun bayyana cewar matukar gwamnoni ba su kawo karshen asusun hadin guiwa ba, to yankunan karkara za su ci- gaba da zama a mace.

Babu hanyoyin mota masu kyau domin sun koma ramuka da laka musamman a lokacin damina, makarantu sun lalace, ba kujeru ba malamai ballantana kayan aiki, haka ma asibitoci sun tabarbare, ba gina mai kyau, ba magani, ba kuma kwararrun likitoci, ruwan sha kuwa gurbatattu ne a mafi yawan yankuna.

“Muna cike da da juyayin yadda muke rayuwa a cikin mawuyacin hali duk da cewa a na raba biliyoyin naira kowanne wata daga Abuja da sunan kananan hukumomin mu, amma kuma babu aikin nunawa na ko miliyan 50.” In ji Dalha Bagega.

A bayyane yake cewar shugaban karamar hukuma a yau ya zama tamkar mai jiran albashi ba tare da ikon gudanar da matsakaita da manyan ayyukan raya kauyuka ba. Hakan ya kawar da amincewar jama’a da tsarin mulkin dimokuradiyya ta yadda shugabannin da aka zaba ke zama ’yan amshin shatan gwamnoni.

Majalisun kananan hukumomi sun jima da zama tamkar makabarta, duk da dimbin ma’aikatan da ke ga kananan hukumomi amma ‘yan kwarorin ma’aikata kawai ake gani a sakatariya, galibi daga albashi sai albashi majalisun ke cika.

A bayyane yake cewar wasu shugabannin kananan hukumomi na samun kananan kudade ne kawai, wani lokaci kasa da miliyan 5 a wata, duk da cewa an ware musu biliyoyin naira wanda hakan ne dalilin da yasa jama’a ke cewa yankunan karkara sun mutu.

Gabanin zaben 2019, a wata muhawara da BBC Hausa ta shirya da ‘yan takarar gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC ya bayyana cewar idan ya samu nasarar zama gwamna zai kawo karshen asusun hadin guiwa tsakanin jiha da kananan hukumomi domin ba su kudaden su kai tsaye su gudanar da ayyuka.

Ya ce “Shugaban karamar hukuma ba ya iya gyara abincin gidansa ballantana daraktan karamar hukuma, idan ma’aikacin karamar hukuma ya tashi ba ya iya zuwa aiki domin sakatariya a rufe take, shugaban karamar hukuma ba ya zama, darakta ma ba ya zama, duk sun dawo cikin gari, kowa yawo, kowa ba ya da abin yi, an kashe ko’ina da ko’ina, don haka za mu tabbatar mun baiwa kananan hukumomi damar ‘yancin gashin kan su, za mu ba su dama su yi ayyuka.” in ji Aliyu.

Sai dai a sama da shekaru biyu na mulkinsa, har yau Gwamna Ahmad Aliyu ya kasa cika alkawalin da ya dauka domin kuwa matsayin kananan hukumomi na nan a yadda yake ba tare da sakar masu mara sun samu ‘yancin gashin kai ba kamar yadda ya bayyana kafin hawa kujerar mulki.

Malama Aishatu Bello daga Ungushi ta bayyana cewar “Mun fi shekara biyar ba mu ga aikin gwamnati a nan ba. Rijiyar da aka yi ta lalace, asibiti babu magani, makarantar yara ta zama karkashin bishiya.”

A Karaye, wani manomi mai suna Malam Tasi’u ya bayyana cewar “Mun fi jin gwamnati a rediyo fiye da gani da ido. Yara na karatu babu allo, ba kujeru.”

Ire- iren wadannan kalaman na bayyana irin radadin da talaka ke ji, saboda rashin samun wani jin dadi ko kulawa daga gwamnatin da hakkin su ya rataya a wuyan ta.

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya ta bayyana cewa tsarin biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye gare su na iya “kwace ikon jihohi daga hannun su.” Shugaban kungiyar, Abdulrahman Abdulrazak na Kwara, ya bayyana cewar hakan zai iya karya tsarin dimokuradiyya.

Sai dai masana doka sun ce hujjar ba ta da tushe domin Kotun Koli ta riga ta fayyace cewa kudaden kananan hukumomi ba mallakin gwamnoni ba ne, don haka wajibi ne a ba su hakkin su.

A kan wannan kungiyar kwadago a Nijeriya ra bayyana cewar rashin bin hukuncin kotu ya zama cin zarafi ga tsarin mulkin kasa. Ta ce ba daidai ba ne yadda Gwamnoni ke tauye hakkokin jama’a.

Ra’ayin kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi a bayyane yake a bisa ga yadda suka bayyana cewar idan aka ba su kudinsu kai tsaye, za su dawo da kwarin gwiwa wajen yi wa jama’a hidima. Hasalima sun yi yajin aiki a lokuta da dama kan wannan matsalar.

Tuni dai kungiyoyin farar hula kamar SERAP da BudgIT suka gargadi gwamnonin jihohi da cewar duk gwamnan da ya ci- gaba da rike kudin kananan hukumomi shi ne ke kashe karkara da hannun sa.

Daga cikin jihohi, Gwamnatin Katsina ta zama ta farko a Nijeriya da ta bayyana cewa za ta kawo karshen asusun hadin guiwa tsakanin jiha da kananan hukumomi ta hanyar tura kudaden kai tsaye daga watan Satumba 2025.

Wannan ya sa ake yabawa Gwamna Dikko Umar Radda kan daukar matakin raya kananan hukumomi. A haka Katsina ta zama matsayin jihar gwaji wajen tantance ko tabbatar da tsarin zai yi tasiri ko akasin hakan.

Idan aka fara biyan kudaden kai tsaye, akwai kalubalen da za a fuskanta da suka hada da rashin cancantar shugabannin kananan hukumomi da barazanar cin hanci da rashawa.

Sai dai masana sun jaddada cewa baiwa kananan hukumomi gashin kan su ya fi zama alheri fiye da tsarin da ke hannun gwamnoni domin a kalla talaka zai iya hisabi da shugabannin da ke kusa da shi.

Batun ’yancin kananan hukumomi ya riga ya zama jarabawa ga dimukuradiyyar Nijeriya. Idan aka aiwatar da shi yadda doka ta tanada, rayuwar al’ummar karkara za ta samu sauyi mai ma’ana: makarantu za su dawo da martaba, asibitoci za su cika da kayan aiki, hanyoyin mota za su inganta kuma za a samu ruwan sha masu tsafta.

Amma idan a ka ci- gaba da barin gwamnoni na mallake kudaden kananan hukumomi, to za a ci- gaba da ganin al’amurra tabarbare a karkara. Talakawa za ci- gaba da zama marayu a cikin tsarin dimukuradiyyar da aka ce an gina domin su.

Tambayar ita ce: shin baya ga jihar Katsina da ta dauki hanyar zama zakaran gwajin dafi, shin sauran gwamnoni za su yi adalci ga kananan hukumomi ko kuwa za a bar su har abada a cikin kangin gwamnoni?


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KatsinaƘananan Hukumomi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa

Next Post

Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura

Related

NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba
Manyan Labarai

NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba

3 hours ago
Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa
Manyan Labarai

Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa

6 hours ago
Ya Kamata Karancin Malamai A Duniya Ya Zama Darasi Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Ya Kamata Karancin Malamai A Duniya Ya Zama Darasi Ga Nijeriya

7 hours ago
Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace

16 hours ago
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
Al'ajabi

Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano

19 hours ago
Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda
Manyan Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Bankaɗo Ma’aikatan Bogi 3,488

21 hours ago
Next Post
Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura

Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura

LABARAI MASU NASABA

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

September 26, 2025
Goron Sallah

GORON JUMA’A

September 26, 2025
NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba

NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba

September 26, 2025
Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar

Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar

September 26, 2025
Manyan Ƴan Siyasa Sun Yi Watsi Da Kafa Sabuwar Jam’iyyar ADA Sun Rungumi ADC

Manyan Ƴan Siyasa Sun Yi Watsi Da Kafa Sabuwar Jam’iyyar ADA Sun Rungumi ADC

September 26, 2025
Manyan Motoci 2,000 A Kullum Ke Zirga-zirga A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Jihar Legas —Rahoto

Manyan Motoci 2,000 A Kullum Ke Zirga-zirga A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Jihar Legas —Rahoto

September 26, 2025
Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura

Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura

September 26, 2025
‘Yancin Kananan Hukumomi: Yadda Gwamnoni Suke Kawo Cikas

‘Yancin Kananan Hukumomi: Yadda Gwamnoni Suke Kawo Cikas

September 26, 2025
Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa

Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa

September 26, 2025
Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

September 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.