Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama da kuma martani daga ƙungiyoyin addinin Musulunci kan kalaman da Sheikh Lawan Triumph ya yi kwanan nan a jihar.
A cewar sanarwar da ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar ta fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Musa Tanko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a miƙa batun ga Majalisar Shura ta Jihar Kano domin yin nazari da tattaunawa.
- Yawan Kudin Da Aka Kashe Na Zamantakewa A Watan Agusta A Kasar Sin Ya Kai RMB Triliyan 3.97
- Tinubu Ya Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Babban Ɗan Jarida Kabir Yusuf
Ƙungiyoyin da suka shigar da ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da Safiyatul Islam of Nigeria, da Tijjaniya Youth Enlightenment Forum, da Interfaith Parties for Peace and Development, da Sairul Qalbi Foundation, da Habbullah Mateen Foundation, da Limaman Masallatan Juma’a ƙarƙashin Qadiriyya Movement, da Kwamitin Malaman Sunnah na Kano, da kuma Multaqa Ahbab Alsufiyya.
Sakataren Gwamnati, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce gwamnatin jihar ta jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya, da haɗin kai da mutunta juna tsakanin dukkan ƙungiyoyin addini, tare da kira ga jama’ar Kano da su kasance cikin kwanciyar hankali kuma su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tashin hankali ba.