Ana hasashen cewa farashin man fetur zai iya ƙaruwa a Nijeriya bayan da Matatar Man Dangote ta sanar da cewa daga ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, ba za ta sake sayar da mai ga ƴan kasuwa da Naira ba.
Wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Juma’a ta ce kwastomomin da suka riga suka biya da Naira za su iya neman a mayar musu da kuɗaɗensu. Wannan mataki ya sake tayar da muhawara kan tasirin harkar mai ga tattalin arziƙin Nijeriya.
- Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG
- Mun Kawo Ƙarshen Dogon Layin Mai Na Shekara 50 A Nijeriya – Matatar Dangote
Wannan ba shi ne karo na farko da matatar Dangote ta ɗauki irin wannan mataki ba. A watan Maris na shekarar 2025, kamfanin ya dakatar da siyar da mai da Naira tare da sanar da cewa zai karɓi Dala ne kaɗai, lamarin da ya janyo suka dagawa masana da al’umma hankali.
Sai dai a halin yanzu, ƙungiyar masu kasuwar nakamashi ta Nijeriya (MEMAN) ta roƙi ‘yan ƙasa da kada su tayar da hankali, tana mai cewa akwai tattaunawa a tsakanin ɓangarorin. Babban Sakataren ƙungiyar, Mista Clement Isong, ya ce ba za a iya siyar da man fetur a Nijeriya da Dala ba, ya kuma bada tabbacin cewa matsalar za ta sami mafita nan ba da jimawa ba.
Masana harkar tattalin arziƙi sun ce, idan wannan matakin ya ɗore, zai iya jefa ƴan kasuwa da masu amfani da man fetur cikin ƙarin tsadar rayuwa, kasancewar yawancin ma’amaloli da sufuri na dogara ne ga farashin mai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp