A garin Aral, dake dab da hamada a tsakiyar jihar Xinjiang ta kasar Sin, akwai dimbin itatuwan Hu-Yang, ko Populus Euphratica a Turance, da fadin filinsu ya kai dubban kadada. Saboda hanyar kogi wadda ta bi wajen wadannan itatuwa a baya, ta karkata zuwa sauran wurare, sama da shekaru 400 da suka gabata, don haka wadannan itatuwa sun bushe sosai, tamkar sun riga sun mutu. Sai dai da zarar saiwoyinsu sun sami dan ruwa kadan, to, nan take sai su farfado, su fara toho, da fitar da sabbin rassa da ganyaye, kamar yadda bishiyar Hu-Yang da na dauki hotonta take.
Matsanancin yanayin hamada ya haifar da juriyar bishiyar Hu-Yang, da ruhin mutanen wurin na matukar jure wa wahalhalu.Jim kadan bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekara ta 1949, wani reshen rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin ya shiga yankunan hamada na Xinjiang, inda suka fara tsaron wurin da gudanar da aikin gona a can. Sun gina matsuguni a dab da hamadar Taklimakan, da haka magudanan ruwa, da gina dimbin tituna, da mai da sauruka filayen gona, tare da kafa wasu sabbin garuruwa da dama, ciki har da Alar, wanda na ziyarta a kwanan baya. A cikin garin, na ga kyawawan tituna, da dimbin itatuwa da bishiyoyi, da manyan gine-ginen gidajen zama, da masana’antu na zamani, da kuma wata babbar jami’a mai dalibai da malamai kimanin 40,000, wadda har yanzu ke kokarin ci gaba da samun habaka. Bisa yanayin wurin, zai yi wuya mutum ya yi tunanin cewa, kimanin wasu shekaru 70 da suka gabata, kusan babu wani abu a wannan wuri, illa hamada da kasa mai gishiri.
Kamar yadda bishiyar Hu-Yang ke kokarin neman ruwa a cikin muhalli wajen rayuwa da girma, mutanen Alar kuma suna iyakacin kokarin raya tattalin arziki. Da suka ga yadda kasa ta kunshi gishiri da yawa, sai su fara noman shinkafa, inda suke amfani da damar ban ruwa wajen wanke gishiri daga cikin kasar. Bayan sun girbi shinkafar, sai su shuka auduga, da alkama, da masara. Kana ruwa mai gishiri da aka samu ta hanyar wanke kasa ma, ba za a salwatar da shi ba, inda ake tattara shi, da daidaita yanayin gishirinsa, sa’an nan a sake amfani da shi wajen kiwon kifi da jatan lande na teku. Hatta yashi na hamada ma ana amfani da shi sosai: Ta hanyar hada shi da tokar kwal, ana samar da wani nau’in kasa da ake iya noman kayan lambu a kanta, wadda ta maye gurbin kasar asali mai gishiri.
Tabbas, ko a zamanin yau ma, aikin raya tattalin arziki ba ya rabuwa da wahalhalu. Misali, a cikin gidajen da ake kiwon jatan lande, dole ne mutane su jure yanayi mai zafi da ya kan kai sama da digiri 40 na ma’aunin Celcius, da kuma tarin sauro dake cizon mutum. Har ila yau, akwai wasu kifayen da ake kiwonsu, misali Mullet, wadanda mazauna yankin Xinjiang ba su saba da cinsu ba, don haka ana bukatar karin kokari a fannin tallarsu a kasuwa.Duk da haka, lokacin da ake magana kan makomar harkokinsu, masu samar da kayan noma na Alar suna cike da kwarin gwiwa. Wani mai kiwon kifi ya bayyana cewa, “Bisa fasahar noman abincin ruwa da muka bunkasa a nan, za mu iya kiwon kifaye a duk inda muke so.” Kana a nasa bangare, shugaban wani kamfanin noman shinkafa ya yaba da albarkatun noma na jihar Xinjiang, inda ya ce, da yawan kasar da jihar ke da shi, da tsawon lokacin maras kankara, da kuma yawan hasken rana, jihar ta zama daya daga cikin wurare mafi dacewa da raya aikin gona.
Ci gaban Alar wani misali ne na ci gaban daukacin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, bayan da aka kafa ta shekaru 70 da suka gabata. Albarkacin matukar hakuri da juriya, da suka yi kama da halayyar bishiyar Hu-Yang, da yadda ake amfani da dukkan albarkatun da ake iya samu wajen neman ci gaba a cikin lokaci mai tsawo, jihar Xinjiang da ke yankin kan iyakar kasar Sin, ta tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kan kabilu daban daban, da zama cibiyar kasuwanci da ke hada Asiya da Turai, da kuma babbar cibiyar dake samar da kayayyakin masana’antu iri-iri. Kana jimillar GDPn jihar ta karu da fiye da ninki 1,600 tun daga shekarar 1955, abin da ya sa mazauna jihar bayyana cewa, “Rayuwa a yau ba ta misaltuwa da ta baya.”
A halin yanzu, albarkacin kokarin da ake yi na hakar magudanar ruwa da sake amfani da ruwa mai gishiri da aka samu bisa wanke kasa mai gishiri yayin da ake gudanar da aikin noma, wajen ban ruwa a cikin hamada, dimbin itatuwan Hu-Yang na Alar sun koma kore kuma suka fara toho. Hakan na alamanta kyakkyawar makoma ta jihar Xinjiang. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp