Kwamitin majalisar wakilai mai kula da albarkatun man fetur na kasa ya dakile umarnin da kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya (PENGASSAN) ta fitar, inda ta umurci wasu rassanta da su dakatar da bai wa matatar man Dangote iskar gas da ɗanyen mai biyo bayan rikicin dake tsakaninta da mahukuntan matatar.
Kwamitin majalisar ya ce matakin na PENGASSAN ya kauce tsarin kundin dokar da aka kafa kungiyar ‘yan kasuwa, don haka, ya yi kira ga kungiyar masu zanga-zangar da ta ɗage wannan umarni tare da barin kofar tattaunawa don samar da mafita.
A cewar shugaban kwamitin, Hon. Ikenga Imo Ugochinyere, yayin ganawa da manema labarai a Legas, ya ce rikicin masana’antu, wanda ya haifar da umarnin katse samarwa kamfanin mai na ‘yan asalin kasar – Dangote albarkatu, zai kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasa kuma zai tsoratar da masu zuba jari daga kasar nan saboda an ba da umarnin cikin gaggawa ba tare da samar da duk wata hanyar magance koke-kokensu (PENGASSAN) ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp