Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta gudanar da zaɓen shugabanni na jiha, inda ta zaɓi sabbin shugabanni da za su jagoranci harkokin jam’iyyar a jihar.
A yayin taron da aka gudanar a Ilorin ranar Asabar, an bayyana Hon. Adamu Bawa Isa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar, inda ya samu ƙuri’u 1,498 daga cikin wakilai 1,572 da aka tantance.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Fasinjoji 8 Da Aka Sace A Kogi
- APC Da PDP Na Zargin Juna Kan Amfani Da Addini Wajen Neman Nasara A 2027
Sauran sabbin shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da: Mrs. Wasilat Macarthy (mataimakiyar shugaba), da Malam Abdullahi AbdulRahman (sakataren jam’iyya), da Rev. Cornelius Fawenu (ma’aji), da Hon. Umar Shero (sakataren kuɗi), da Olusegun Olushola (sakataren yaɗa labarai), da Barr. Monsurat Omotosho (mai ba da shawara a fannin doka), da kuma Musa Bashir (mai binciken kuɗi).
Hukumar gudanar da zaɓen jam’iyyar ta ƙasa ta bayyana wannan zaɓen na Kwara a matsayin abin koyi ga tsarin zaɓe mai inganci. Wakilin hukumar, Jacob Mark, ya ce taron ya gudana kamar “zaman iyali” mai cike da fahimtar juna.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin zaman lafiya da adalci, inda ya ce: “PDP ta sake tabbatar da cewa ita ce jam’iyyar da ke samar da daidaitacciyar dama, tare da fifita muradin jama’a.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp