Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bai wa tawagar ƴan ƙasa da shekaru 20 ta mata ta Nijeriya (Super Falconets) kyautar dala 15,000 (kimanin Naira miliyan 22) bayan nasarar da suka samu akan Rwanda da ci 4-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ƙasa da shekaru 20 da za a yi a 2026. An dai buga wasan a filin wasa na Lekan Salami, Ibadan, ranar Lahadi.
Precious Oscar, da Tumininu Adeshina, da Janet Akekoromowei da Alaba Olabiyi ne suka zura ƙwallaye huɗu da suka tabbatar wa Falconets nasara a wasan. Bayan haɗa sakamakon wasanni biyu da aka buga tsakaninsu da Rwanda, Nijeriya ta doke abokiyar karawarta da ci 5-0 baki ɗaya. Falconets yanzu za su fafata da Senegal ko Algeria a zagaye na uku a watan Fabrairun baɗi.
- Majalisa Ta Daƙile PENGASSAN Akan Shirin Daina Kai Wa Matatar Ɗangote Gas Da Ɗanyen Mai
- Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin Naira
Da yake miƙa kyautar kuɗin, Gwamna Makinde ya ce: “Jajircewa da kishin ƙasa ne ya kawo wannan nasara. Ina ƙarfafa muku gwuiwa da ku ci gaba da nuna bajinta har ku lashe manyan gasa, kamar yadda Super Falcons suka yi a gasar Afrika ta mata a Masar.”
Falconets, waɗanda ke fatan kai wa gasar cin kofin duniya a 2026, sun yi godiya ga gwamnan bisa wannan tallafi. Sun kuma tabbatar da cewa za su ci gaba da dagewa wajen samun manyan nasarori a matakan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp