Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta sake yin sabon gargaɗi kan yiwuwar samun ambaliya bayan hasashen da ta yi a ranar 29 ga watan Satumba, 2025.
A wata takarda da Daraktan Sashen Kula da Kwazazzabai, Ambaliya da Yankunan Gaɓar Ruwa, Usman Abdullahi Bokani, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa ana sa ran ruwan sama mai yawa tsakanin 1 zuwa 3 ga watan Oktoba, 2025, wanda ka iya haddasa ambaliya.
- PSG Ta Doke Barcelona Har Gida A Gasar Zakarun Turai
- Murnar Zagayowar Ranar Kafuwar Kasar Sin: Bikin Bana Na Daban Ne
Jihohin da ambaliyar ka iya shafa sun haɗa da Adamawa, Kebbi, Bauchi, Zamfara, Sakkwato, Kaduna da Neja.
Kebbi ce ke da mafi yawan wuraren da aka fi sa ido, ciki har da Argungu, Bagudu, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa da Birnin Kebbi.
Kaduna ce ke da mafi ƙaranci da Jaji da Zariya kawai, yayin da a Jihar Neja aka sanya Magama da Sarkin-Pawa.
Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare.
Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci.
Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa da koguna ko rafuka su ɗauki matakan kariya ko su bar waɗannan wurare domin guje wa ambaliyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp