Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade, ya roƙi gwamnatin tarayya ta matsa ƙaimi wajen ganowa da kuma kama masu hannu a kashe-kashen da suka auku a wasu yankunan Kwara domin fuskantar hukunci. Ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su haɗa kai wajen tunkarar waɗanda ya kira “masu shan jinin jama’a”, waɗanda suke jin daɗi da kisan rayukan marasa laifi.
Oba Owoade ya bayyana cewa hukunta waɗannan miyagun zai ƙarfafa haɗin kan al’umma domin kuɓutar da ƙasa daga ƙangin ta’addanci da rashin imani. Ya kuma jaddada cewa dole ne a kiyaye al’adun da ke ɗaukaka girmama rayuwa da mutuncin ɗan Adam, domin kada a miƙa su ga marasa imani.
- Collins Daga BUK Na Dab Da Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie
- Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?
Wannan kira na Alaafin ya biyo bayan kashe wasu ƴan ƙabilar Yarbawa da ake zargin makiyaya Fulani ne suka yi a Oke Ode, jihar Kwara. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen hulɗa da manema labarai, Bode Durojaye, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa Sarkin ya riga ya tuntubi gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRasaq, kan wannan mummunan lamari.
A cewar sanarwar, gwamnan ya tabbatar wa da Oba Owoade cewa an tura dakarun tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da tabbatar da tsaron mazauna yankin. Sarkin ya kuma yi kira ga shugabanni da jama’a gaba ɗaya da su yi gaskiya wajen fuskantar tushen matsalar tsaro da ta ƙunshi aikata laifuka, tayar da ƙayar baya, da kuma ta’addancin makiyaya da ya ƙara tsananta kwanan nan.
Yayin da yake yaba wa hukumomin tsaro bisa jajircewarsu, Alaafin ya yi gargaɗin kauce wa duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya, da daidaito, da haɗin kan ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp