A kwanakin baya, ofisoshin jakadancin Sin dake kasashen Afirka sun gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 76 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, inda manyan jami’an kasashen Afirka suka yaba da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kana suna son fadada hadin gwiwa tare da kasar Sin, da kuma inganta dangantakar dake tsakaninsu da kasar Sin baki daya.
Ministan harkokin wajen kasar Tanzania Mahmoud Thabit Kombo ya bayyana cewa, Tanzania da Sin sun sada zumunta a dogon lokaci, kasar Tanzania za ta kara yin imani da fadada hadin gwiwa tare da kasar Sin don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da amfanar da jama’arsu baki daya.
Ministan harkokin ilmi da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire na kasar Afirka ta Kudu Blade Nzimande ya bayyana cewa, matakin soke harajin kwastam na kasar Sin ya taimaka wa kasar Afirka ta Kudu wajen bunkasa tattalin arziki da zamanantar da kasar, kuma Afirka ta Kudu tana son kara yin mu’amala da hadin gwiwa tare da kasar Sin don ingiza dangantakarsu zuwa sabon matsayi.
Ministan kula da harkokin shugaban kasar Botswana Moeti Mohwasa ya bayyana cewa, Sin ta samu manyan nasarori kan bunkasar tattalin arziki da yaki da talauci, wanda ya burge kasarsa sosai. Kasar Botswana tana son koyi da fasahohi da bunkasar kasar Sin da kara yin hadin gwiwa tare da kasar.
Ministan kula da harkokin dakaru na kasar Senegal Birame Diop ya ce, Senegal da Sin suna kokarin fadada hadin gwiwarsu a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewar al’umma, da al’adu, da wasanni da sauransu, kana an riga an gudanar da manyan ayyukan more rayuwa a kasar, hakan zai taimaka wa kasar Senegal wajen samun bunkasa mai dorewa kan tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Ministar kula da shari’a da harkokin majalisar dokoki da hakkin mata ta kasar Sao Tome and Principe Vera Cravid ta yi kira a maida dangantakar dake tsakanin kasarta da kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin dangantakarsu tana da tarihi mai zurfi da kuma samun ci gaba a zamanin yau. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp