Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake hada Lemon Tsamiya:
- ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu
- ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu
Abubuwan da uwargida za ki tanada:
Tsamiya, citta danya, Suga, filebo :
Yadda za ki hada:
Da farko za ki wanke tsamiya sai ki dafa ta ki tace sannan ki wanke danyar citta sai ki nika ta, sannan ki samu roba mai kyau sai ki tace tsamiya tare da cittar kisa suga da filebo sai ki juya sosai ki sa a firij ko ki sa masa kankara. Asha dadi lafiya.
Hadadden Lemon Shayi:
Abubuwan da uwargida za ki tanada:
Kankana, kokumba, sitoru beri na ruwa, lemo, tea bag, danyar citta, abarba, Lemon juice, na’a na’a.
Yadda zaki hada:
Da farko za ki wanke kankana da danyar citta sai ki nika su, sannan ki tace ki zuba a cikin tukunya, sai ki dora akan wuta ki wanke abarba da kokumba, ki yanka ki zuba a cikin tukunya sai ki sa tea bag dinki a ciki.
Idan ya tafasa sai ki sauke ki wanke lemon sai ki matse a wata roba za ki sami roba me kyau sai ki tace lemon da kika matse da dade-haden lemon shayin a ciki sai ki sa sitoru beri na ruwa da lemon juice a ciki sai ki sa ganyan na’a na’an kadan a ciki za ki ji ya yi kamshi sosai. Asha dadi lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp