Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi magana ne, game da abin da ya shafi bawa kananun yara waya. Inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Yara matasa wadanda shekarunsu ba su wuce shekara goma sha biyu ko sha uku zuwa sha biyar ba, wane irin illoli ko matsaloli ko kuma alfano, ba su wayar hannu take da shi?, Wacce shawara ya kamata a bawa iyaye da kananun yara game da hakan?”.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
- Lamine Yamal Zai Shafe Mako 3 Yana Jinya
- ‘Yansanda Sun Ƙwato Muggan Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 120 A Kano
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya rashin amfanin ya fi amfanin yawa, domin yara da suke da kananan shekaru basu waya zai taba harkar neman ilimin su ma’ana koyo domin za ta ke shagaltar da su sosai akan dukkanin wani abu da zai taimake su a rayuwa. To, shawara ta a nan ita ce ya kamata ko da za a siya musu waya to a tsara musu yadda zasu amfani da ita kuma idan suka saba sharuɗan to a kwace wayar,hakan zai taimaka wajen suna mai hankali wajen gudanar da wasu muhimman abubuwa a rayuwar su baza su shagalta da wayar ba.
Sunana Princess Fatimah Mazadu, Goben Najeriya:
Akwai amfani saboda watarana wani abu zai taso mai muhimmanci, iyayensa ba sa kusa za su saukaka ta hanyar kiransu. Matsalar sa lalacewar karatu, koyan dabi’un marasa kyau da masu kyau, basu ko siya musu ba laifi ba ne, amma dai a tsananta saka musu ido dan gudun baraka da lalacewa. Ya zamo kiran mai amfani ne da karatu za su rika yi da shi, ba tiktok ko Instagram ko Twitter ba. Allah ka shirya mana zuriya, ka sa mu dace.
Sunana Anas Bin Malik Achilafiya, Karamar Hukumar ‘Yankwashi, Jihar Jigawa:
Amfanin bayar da waya ga kananan yara; yana saukaka musu sadarwa ga iyaye, abokai, da sauran su, samun ilimi da bincike ta hanyar intanet. Iya jawo jaraba, ko dogaro da waya. Zai iya bude kofa ga illolin yanar gizo (Shiga shafukan batsa, ko neman kudi ta hanyoyin da addini ya haramta), rage huldar mutum da mutane a zahiri. Shawara a kayyade lokacin amfani da waya, iyaye su saka idanu kan abin da yara ke amfani da shi. A sa hankali kan hadari da kuma amfani da ita wajen ilimi da sadarwa mai amfani.
Ubangiji Allah ka kara shirya mu, da zuri’armu shirin addinin musulunci. Allahumma Amin.
Sunana Aisha T. Bello, Jihar Kaduna:
Mahimmancin bawa yara waya shi ne; za su iya bincike kan abin da ya shafi karatunsu. Illar bawa yara masu karancin shekaru waya na da yawa; za su iya dauko dabi’u marasa kyau. Shawara yara su yi amfani da waya bisa jagorancin iyaye, waya ta zama hannun iyaye sai yara za su yi amfani da shi a basu kafin a sakar masu a hannunsu, a bari su iya bambancewa tsakanin tsaba da tsakuwa.
Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga A Jihar Jigawa:
A gaskiya ni a nawa tunanin ba shi da wani amfani, hasali ma bata tarbiyya yake wajen bawa yara wayar hannu. A shawarance iyayen yara su kula sosai wajen basu wayar hannu, domin tana hana yara karatun addini dana zamani mai makon su mayar da hankali wajen karatu to, sai su buge da kallon finafinan hausa musamman ‘series film’.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:
Babu wani alfanu, masu manyan shekaru ma ya ya aka cika bale yara ‘yan mitsitsina?, duk da wani lokacin sanda yaron zai dauki wayar baka sani ba sam, wasu kuma iyaye ne suke siyawa yaran wai gudun kar su taba musu tasu. Babban matsala ce duba da yadda zamani ya lalace lokacin da za a koyawa yaranka saka da mugun zare baka sani ba sai abin ya yi nisa, gyaruwarsa da wuya sai iyaye kuma a shiga wani hali. Babbar shawara a nan in ya zama dole sai yara sun rike waya, ita uwa sai ta kula sosai. Sannan in group ne na makaranta ta saka musu a tata wayar in wani aiki ne dai ta bada tata ayi kawai, Allah ya gyara mana yara ya kuma shirya mana su, Amin.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, A Jihar Filato:
A fahimta ta inda illar take da tasiri shi ne bai wa yara babbar waya, don su rika aikin makaranta ko gogayya da sauran yaran manya. Iyaye masu arziki sun fi yin wannan kuskuren a wajen su hakan ba laifi ba ne, suna ganin hakan yana sa yara su saba da tafiya da zamani. Sai dai a ganina kuskure ne, yara su saba da amfani da babbar waya tun ba su gama balaga ba, kwakwalwar su ba ta kai yadda za su yi wa kansu tunani mai kyau ba. Sakamakon yadda wasu marasa tunani ke amfani da waya ko zaurukan sada zumunta da ake samu ta manyan wayoyi, suna tura abubuwan wadanda ka iya bata tarbiyyar yara. Amma ana iya ba su karamar waya da za su yi amfani da ita, don amsa kira.
Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:
Akwai illah, babu illah. Illar ita ce, shige-shigen Tiktok, Instagram, da sauransu. Yara sun saba da kide-kiden shiga media suna ganin irin abubuwan da ake yi to, zuciya ba ta da kashi wani yaron yana iya zuwa ya ga abin da zai ga kamar burgewa ne, ya je ya fadawa kansa wani yanayi. Amfaninta kuma waya da ita ake harkokin ilimi, musamman idan yaro zai yi karatu wajen gogulin. Fatan mu shi ne Allah ya shirya mana yara.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano LGA, Jihar Kano:
Gaskiya a nawa fahimtar ba shi da amfani, idan ma akwai amfanin bai fi 2% cikin dari ba, in har ya kai kenan. Saboda ba ma iya yara ba, yanzu har da manya waya tana taka rawa sosai wajen koyar da yadda ake aikata wasu miyagun ayyukan, da kuma haddasa karairayi da gurbata tarbiyya da sauransu. Shawarata, idan ma ta kama ana bawa ire-iren wadannan yaran waya to, ya zamana akwai takaitaccen lokaci wanda za a rika karbe wannan wayar. Sannan kuma iyaye su rika binciken wayar, su wa wadannan yaran suke mu’amala da su da kuma me da me suke yi..
Sunana Zulaihat Adamu, Jihar Kaduna:
Gaskiya babu wata matsalar bayar wa, matsalolin basu taka kara sun karya ba. Saboda yanzu komai ya koma amfani da na’ura don cigaban al’umma, malamai da wasu makarantun suka mayar da aikinsu kan waya dan saukakawa. Shawara, shi yaron ya san dan me aka bashi wayar da kuma amfaninta a gurin shi, da tsara lokutan amfani da wayar a gareshi, dan yawan amfani da wayar ka’iya kashe idanuwa cikin sauki, kada a zo garin neman gira a rasa ido.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp