A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Bangladesh Mohammed Shahabuddin sun yi musayar sakon taya murna kan cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
A cikin sakonsa, Xi ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya a shekaru 50 da suka gabata, ba tare da la’akari da sauye-sauyen yanayin kasa da kasa da na shiyya-shiyya ba, Sin da Bangladesh sun kulla huldar abokantaka bisa ka’idoji guda biyar na zaman tare cikin lumana, tare da nuna misali wajen mutunta juna, da daidaito, da hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare a tsakanin kasashen.
Shugaban kasar Sin ya jaddada cewa, a shirye yake ya yi aiki tare da Shahabuddin, wajen ci gaba da sada dadadden zumuncin kasashensu, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna, da karfafa samun ci gaba tare, ta yadda za a amfanar da jama’ar kasashen biyu yadda ya kamata, da ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya.
A nasa bangaren, Shahabuddin ya bayyana cewa, kasar Bangladesh tana matukar godiya da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata ta bai-daya, ya kuma bayyana imanin cewa, bisa kokarin hadin gwiwa na shugabanni da jama’ar kasashen biyu, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen zai haifar da manyan kyawawan sakamako. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp