Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta bayyana damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar ƙarancin malamai a duniya, tana kira da a gaggauta ɗaukar matakai na ɗaukar sabbin malamai, da horar da su, da kuma tallafa musu domin ci gaban sana’ar koyarwa.
A cikin sakonta na taya murna yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2025 mai taken “Mayar da Hankali Kan Ƙarancin Malamai a Duniya,” Uwargidan ta ce wannan matsala tana buƙatar a magance ta cikin gaggawa ta hanyar ƙarfafa wa malamai gwuiwa ƙarfi da kuma dabarun samun ƙwarewa.
- Remi Tinubu Ta Bai Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa A Neja Tallafin N1bn
- Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Ta bayyana malamai a matsayin “gwarazan al’umma”, tana yabawa da rawar da suke takawa wajen gina tunanin yara, da zamar da mafarkan ɗalibai su zama gaskiya, da shiryar da ƙarni masu zuwa, tare da kiran a ƙara darajar tasu a matsayin ginshiƙan makomar ƙasa.
Remi Tinubu, wadda ita ma ta taɓa zama malama, ta ce: “Ina taya ku murna a wannan rana ta musamman. Barkanmu da Ranar Malamai ta Duniya ta 2025.” Ta kuma jaddada buƙatar mayar da hankali kan ƙarfafa sana’ar koyarwa da zuba jari don magance ƙarancin malamai da haɓaka martabar aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp