Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kwara United ta tabbatar da rabuwa da babban Kocinta, Tunde Sanni, bayan rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a wasan gida da Abia Warriors da ci 1-0 a mako na bakwai na gasar Nigeria Premier Football League (NPFL) da aka buga ranar Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa, korar Tunde Sanni ta samo asali ne daga matsin lamba da ya ƙaru bayan ficewar ƙungiyar daga gasar CAF Confederation Cup, inda Afonja Warriors suka fice da jimillar ci 5-3 a hannun Asante Kotoko daga ƙasar Ghana.
- Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars N2m, Ta Dakatar Da Ɗan Wasanta
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, an bayyana cewa an umarci mataimakin Kocin, Ashifat Suleiman, da ya ci gaba da jan ragamar ƙungiyar har sai an naɗa sabon Koci a nan gaba.
Ashifat Suleiman dai ya taɓa riƙe muƙamin babban Koci na wucin gadi kafin a naɗa Tunde Sanni a farkon wannan shekarar.
Ƙungiyar ta bayyana godiya ga Sanni bisa gudummawar da ya bayar ga ci gaban Kwara United, tare da fatan alheri a fagen horar da ƴan wasa a nan gaba.