An ɗage sauraron ƙarar da Ministan Kirkire-kirkire, da Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya shigar a kan Jami’ar Nijeriya Nsukka (UNN) bayan lauyoyin jami’ar sun kasa mika bayanansu a kan lokaci a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Mai shari’a Hauwa Yilwa ce ta ɗage shari’ar zuwa ranar 10 ga Nuwamba, sakamakon tsaiko da aka samu saboda gazawar lauyoyin wadanda ake ƙara wajen mika takardunsu yadda doka ta tanada.
- Rudani Ya Kunno Kai Yayin Da INEC Ta Ki Amincewa Da Shugabancin ADC
- Kotu Ta Kori Buƙatar Ministan Tinubu Na Hana Fitar Da Takardun Karatunsa
Nnaji ya shigar da ƙarar ne bayan zarge-zargen da ake masa kan yin amfani da takardar bogi ta kammala makarantar UNN, wanda ya haifar da cece-kuce a kafafen yada labarai.
A cikin takardun kotu, Ministan yana neman umarnin hana jami’ar boye bayanan karatunsa tare da tilasta su fitar masa da sakamakonsa na ƙarshe (transcript).
A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1909/2025, an haɗa da Ministan Ilimi, da Hukumar Kula da Jami’o’i (NUC), da Jami’ar UNN, da Shugaban Jami’ar Farfesa Simon Ortuanya, da wasu jami’an jami’ar a matsayin waɗanda ake ƙara.
A zaman da aka yi a yau, lauyan Ministan ya shaidawa kotu cewa an isar da takardun shari’ar ga dukkan waɗanda ake ƙara, yana mai zargin Shugaban Jami’ar UNN da saɓa umarnin kotu ta hanyar rubuta wasika ga jaridar yanar gizo Premium Times, inda ya ƙalubalanci ikirarin Nnaji na cewa tsohon ɗalibin jami’ar ne.
A cewar lauyan, wannan wallafa ta karya umarnin kotu na barin komai a yadda yake har sai an saurari shari’ar.
Sai dai lauyan jami’ar ya musanta yin wani kuskure, amma ya ce za su ja hankalin jami’an su don bin umarnin kotu yadda doka ta tanada.