Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ‘yan bindiga a jihar.
Yayin ziyararsa zuwa garin Isanlu-Esa a ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma, inda aka kai hare-hare kwanan nan, Ododo ya gargaɗi duk wanda ke da hannu ko taimak wa masu laifi cewa zai fuskanci hukunci mai tsanani.
- Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
- Nazari Ya Gano Falalen Dutse Na Yanki Mai Nisa A Duniyar Wata Ya Fi Tsananin Sanyi Fiye Da Na Yanki Na Kusa
Ya yaba wa jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ‘yansanda, DSS, da sauran hukumomi bisa jarumtarsu, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa musu don kare al’umma.
Gwamnan ya kuma gargaɗi sarakunan gargajiya da su daina bai wa baƙin mutane fili ba tare da tantance su ba, ind aya bayyana cewa duk mai lasisin haƙar ma’adinai dole ne gwamnati da jami’an tsaro su bincike shi.
Ododo, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a hare-haren, tare da girmama jami’an tsaro da suka rasu.
Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da shugabannin tsaro bisa goyon bayansu wajen yaƙi da rashin tsaro a Kogi.