Yau Juma’a, sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Kim Jong Un, sakatare janar na jam’iyyar Kwadago ta Korea ta Arewa (WPK), kuma shugaban kasar, bisa cikar jam’iyyar ta WPK shekaru 80 da kafuwa.
Shugaba Xi ya yi fatan karkashin jagorancin WPK dake karkashin shugaba Kim Jong Un, Korea ta Arewa za ta ci gaba da daukaka ra’ayin gurguzu da samun sabbin nasarori, tare da fatan kasar za ta gudanar da babban taron jam’iyyar na 9 cikin nasara.
Ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Korea ta Arewa wajen karfafa tuntubar juna da zurfafa hadin gwiwa da raya dangantakarsu, ta yadda za su hidinmtawa ra’ayin gurguzu na kasashen biyu da bayar da kyawawan gudunmuwa ga zaman lafiya da wadata da ci gaban shiyyarsu da ma na duniya.
Bugu da kari, Xi Jinping ya yi wa jam’iyyar WPK fatan samun karin nasarori, yana mai fatan abotar Sin da Korea ta Arewa za ta dore har abada. (Fa’iza Mustapha)
 
			




 
							








