• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya

by Shehu Yahaya and Sulaiman
5 hours ago
Kwastam

Guguwar ritaya mai karfi za ta girgiza Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) a shekarar 2026, yayin da jami’ai 825 za su bar aiki bisa ka’idar ritaya, kamar yadda jaridar LEADERSHIP Hausa ta gano.

 

A watan Agusta na shekarar 2025 rahotanni sun bayyana cewa akalla jami’ai 791 na hukumar za su yi ritaya a shekarar 2026, Sai dai kamar yadda aka zata, adadin ya karu zuwa 825, karin mutum 34, bisa jerin sunayen da hukumar ta sanya suna: “Jerin karshe Na Jami’ai Da Ma’aikata Don Ritaya A Shekarar 2026.

  • Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
  • Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Wannan adadi ya zama babba idan aka kwatanta da yawan ma’aikatan hukumar gaba daya da ke kusan 18,000 a fadin kasar nan wanda ya yi kasa sosai da 30,000 da Majalisar Tarayya ta tsara a matsayin adadin da hukumar ke bukata.

 

LABARAI MASU NASABA

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Wannan lamari ya haifar da tambaya kan yiwuwar dorewar shirin sauye-sauye da na zamani da ake gudanarwa a karkashin jagorancin Babban Kwanturola Janar, Adewale Adeniyi.

 

Adewale Adeniyi, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara wa wa’adin mulki na shekara guda, shima zai yi ritaya daga hukumar a watan Agusta, 2026.

 

A halin yanzu, za a dauki babban mataki kafin a cike gibin ma’aikata da ake bukata a hukumar kwastam, musamman idan aka yi la’akari da cewa jami’ai 825 za su bar aiki ba tare da sabon daukar ma’aikata ba.

 

Binciken da leadership Hausa ta gudanar ya gano cewa ritayar ta shafi kowane mataki a hukumar daga manyan shugabanni, zuwa matsakaita, har da kananan jami’ai.

 

Daga cikin jami’ai 825 da za su yi ritaya saboda shekaru 60 da suka kai ko kuma shekaru 35 na aiki:

 

5 suna da mukamin mataimakan kwanturola na kasa wato (DCG) sai wasu kananan mataimaka Kwanturola na kasa (ACG) su 13 sai kuma Kwanturololi ( CAC) guda 53 da mataimakanau (DC) guda 51 kananan mataimaka Kwanturola ( AC) guda 46.

 

Sauran sune ; masu mukaman (CSC) guda 61 sai ( SC) Guda 226 da ( DSC) su 285 sai (ASC I) 64 da (ASC II) su 10 (IC), su 8 (CA I) guda 1 sai (CA II) su 2 Jami’an mataimaka Kwanturola Janar ( DCG) guda biyar da ritayar ta shafa su ne: Mista C.K. Niagwan da K.I. Adeola da kuma Mista S. Chiroma; Mr. G.M. Omale; da Mista A. Nnadi.

 

Kananan Jami’an mataimaka Kwanturola Janar (ACG) guda goma sha uku (13) da abin ya shafa su ne: K.C. Egwuh, M.S. Yusuf, da Z.M. Gaji da N.P. Umoh da O.A. Adebakin da kuma T. Bomodi da B.O. Olomu, O.P. Olaniyan, I.K. Oladeji, K. Mohammed, O.A. Adebakin, da B. Mohammed, da C.C. Dim.

 

Daga cikin Kwanturololi da za su yi ritaya a 2026, akwai: D. Abubakar, da O.Y. Shuaibu, F.A. Bodunde da P.C. Chibuoke, da kuma O.O. Akingbade, da A. Salihu, da wasu da dama.

 

A matsayin shiri kafin ranar ritayar 2026, Hedikwatar Hukumar Kwastam da ke Abuja ta bayar da umarni ga dukkan jami’an da abin ya shafa su fara shirye-shiryen barin aiki kamin ranar ta isko su.

 

Hakazalika, An umurce su da su mika sanarwar izinin hutu na watanni uku kafin ritaya ga Babban Kwanturola Janar na Kwastam (CGC).

 

A cikin takardar da wakilinmu ya gani mai taken “Jerin karshe Na Jami’ai da Ma’aikata Don Ritaya A Shekarar 2026”, wacce aka fitar ranar 19 ga Satumba, 2025, kuma Kwanturola A.A. Bazuaye ya sanya hannu a madadin DCG na Sashen Albarkatun Dan Adam (HR), an bukaci jami’an da abin ya shafa da su bi doka da tsari.

 

Kamar yadda takardar ta ce: “A bisa Dokar Aikin Gwamnati (PSR No. 100238) da kuma Sanarwar Gwamnati mai lamba 36216/S.1/D/T: CR1/2001/5 na 20/3/2001, dukkan jami’an da suka cika shekarun ritaya a 2026 za su bar aiki kuma su tafi hutu na watanni uku kafin ranar da ritayar za ta fara aiki.”

 

Haka kuma, an umurci dukkan jami’an da abin ya shafa su tabbatar da bin umarnin, tare da tura takardar sanarwar hutun ritayarsu ga Babban Kwanturola Janar yadda ya dace.

 

Takardar ta kuma bukaci Koordinetocin Yankuna da Kwamandojin Yankuna su sanar da duk jami’an da abin ya shafa a yankunansu.

 

Da wannan yawan ma’aikata da za su bar aiki a 2026, har yanzu ana cikin tunanin irin dabarar da shugabancin kwastam zai yi amfani da ita don cike gibin da zai biyo baya, tare da tabbatar da ci gaba da sabbin domin gudanar da ayyukan hukumar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nijeriya
Labarai

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)
Labarai

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Next Post
Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya

Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari'a Da Inganta Shugabanci A Duniya

LABARAI MASU NASABA

A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho

October 10, 2025
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

October 10, 2025
peter

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

October 10, 2025
Jonathan

Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole

October 10, 2025
Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka

Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka

October 10, 2025
Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya

Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya

October 10, 2025
Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata  

Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata  

October 10, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

2027: INEC Ta Nemi A Gaggauta Amincewa Da Ƙudirin Sake Fasalin Tsarin Zaɓe

October 10, 2025
Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya

Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.