Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Hannun Jari Dakta Jumoke Oduwole, ta bukaci Hukumomin Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da rinka sayen kayana da ake sarrafawa a cikin kasar nan.
Ta bayar da wannan shawarar ce, bayan da yi na’am da wata mota samfarin Nord da aka hada ta a kasar, inda kuma ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungimi fannin kera motoci a cikin kasar.
- Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe
- CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kai ziyarar aiki kamfanin hada motocin na Nord da ke cikin harabar jami’ar UNILAG da ke a jihar Legas.
Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta.
A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare.
Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da shi, zai iya cike gibin bukatar da ake da ita, ta ‘yan kasar na bukatar motocin.
Ya ci gaba da cewa, za mu ci gaba da kara karfafa kwarin guwair ‘yan kasar domin da kuma sauran kamfanoni masu zaman kansu domin su rinka sayen kayan da kamfanonin kasar, suka sarrafa da kuma hada su.
Ta ce, wannan babban abin alhari ne, ganin cewa, a wannan jami’ar ce, aka hada wannan mortar.
Shi kuwa a na sa jawabin Farfesa Oboh ya bayyana cewa, muna Myrna da wannan shirin na Gwamnatin Tarayya wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ke jagorantar bai wa ‘yan kasar kwarin guwair sayen kayan da aka sarrafa a cikin kasar
A cewarsa, jami’ar ta UNILAG, ba wai kawai na yin alfahari da samun wannan wajen hada motocin ba ne, kadai amma ta na alharin da cewa, an samar da wajen a jami’ar.
Shi ma, Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi, a yayin da ya ke nuna jin dadinsa kan gudunmwar da ministar ke bai wa kamfanin ya a bayyana cewa, na yi matukar farin ciki ganin cewa, ministar ta kasance daya daga cikin abokan cinikayyar mu
Kazalika, Shugaban ya kuma gode wa mahukunta jami’ar ta UNILAG kan yin hadaka da kamfanin.