Babban Jami’in Diflomasiyyar Sin Ya Jaddada Matsayar Dangantakar Kasar Da Turai Ta Hadin Gwiwa
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, ya kamata Sin da Turai su tsaya tsayin daka kan matsayar dangantakarsu ta hadin gwiwa, da kauce wa siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, da kuma zakewa kan batun tsaro a bangaren musaya, da yin aiki wajen samun bunkasar ciniki daidai-wa-daida cikin dogon zango. Wang, wanda kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da tawagar jam'iyyu ta majalisar yankin Turai karkashin jagorancin David McAllister, shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar, a nan birnin Beijing. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















