Babban Hafsan Sojojin Nijeriya ya bayyana cewa dakarun Runduna ta 6, Sashen 3 na Ayyukan “Whirl Stroke (OPWS)”, tare da hadin gwiwar jami’an ‘yansanda, sun samu nasarar ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, ciki har da yaro daya, da safiyar ranar 2 ga Oktoba, 2025.
A halin da ake ciki, kungiyar Matan Sojoji da ‘Yansanda (DEPOWA) ta gudanar da addu’o’i ga Allah domin kariya ga mazajensu, wadanda ke tsaye daram don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
- Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
- Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
Mai magana da yawun runduna ta 6 na Sojojin Nijeriya, Laftanar Umar Muhammad, ya bayyana cewa an ceto wadanda abin ya shafa ne a wani bangare na ci gaba da aikin share sansanonin ‘yan ta’adda a Jihar Taraba, wanda ake kira “Operation Lafiya Nakowa.”
Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan.
A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton.
Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba.
Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa a ayyukan tsaro da ake gudanarwa a fadin jihar.
A wani labari mai nasaba da haka, Kungiyar Matan Sojoji da ‘Yansanda (DEPOWA) ta yaba da jajircewa da sadaukarwar dakarun rundunonin sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro, wadanda ke ci gaba da sadaukar da rayuwarsu domin kare kasar.
Kungiyar ta kuma yi addu’a ga Allah domin kare mazajensu, wadanda ke kwana suna tashi a kan bakin aiki domin tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya.
Shugabar kungiyar DEPOWA, kuma matar Babban Hafsan Tsaro na Kasa (CDS), Mrs. Oghogho Musa, ta bayyana wannan godiya tare da yin addu’o’i a birnin Abuja yayin gudanar da wasan motsa jiki na rawa (Dance Aerobics Edercise) da aka gudanar a makarantar DEPOWA da ke sansanin Mogadishu.
Shugabar DEPOWA ta kuma jaddada kudirin kungiyar na gudanar da yakin addu’a da godiya na tsawon shekara guda ga dakarun da ke bakin daga, domin nuna yabo da godiya ga jajircewarsu wajen kare kasar Nijeriya, duk da hadarin da ke tattare da aikin.