Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi za su jagoranci wani babban taron zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh na Masar, da nufin samar da dawwamammiyar matsaya kan rikicin Gaza.
Taron wanda aka shirya gudanarwa a karshen wannan mako, zai hada manyan shugabannin kasashen duniya da suka hada da shugaban Faransa, Emmanuel Macron da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wadanda dukkansu suka tabbatar da halartarsu ta ofisoshinsu.
Haka kuma kungiyar Tarayyar Turai za ta samu wakilcin shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa, wanda kakakinsa ya ce kungiyar na goyon bayan shirin.
Sai dai har yanzu ba a san ko Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai shiga tattaunawar ba, saboda babu wani tabbaci a hukumance daga ofishinsa.
Itama ana ta ɓangaren, Hamas ba za ta samu halartar taron ba. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na AFP, Hossam Badran, wani jigo a ofishin siyasa na kungiyar, ya ce ɓangaren Falasdinawa “ba zai shiga tattaunawar ba.”
Badran ya kara da cewa, dama kungiyar Hamas tana samun wakilci ne, daga Qatar da Masar kamar yadda aka yi a tattaunawa game da rikicin Gaza da Isra’ila.