James Shikwati, masanin ilimin tattalin arziki dan kasar Kenya ne mai daukar ra’ayi na “Liberalism”, wanda ya dade yana ba da shawarar magance talauci a Afirka ta hanyar amfani da dabarar ciniki cikin ‘yanci. Watakila sakamakon yadda yake gudanar da bincike da samun fahimta mai zurfi kan tsarin tattalin arziki na “Liberalism”, a kwanan baya ya soki tsarin da kasashen yamma ke kokarin yayatawa a duniya, a cikin wata makala ta baya-bayan nan, yana mai cewa tsarin na gurgunta karfin kasashen Afirka na neman ci gaba.
Cikin makalarsa da jaridar “The Independent” ta kasar Uganda ta wallafa, Mista Shikwati ya ce, bayan yakin duniya na biyu, kasashen yamma sun bayyana tsarin “Liberalism” a matsayin “hanyar neman samun ci gaba ta dole”, tare da dora shi a kan kasashen Afirka, ba tare da la’akari da hakikanin yanayin da suke ciki da al’adunsu ba. Sakamakon wannan mataki, kasashen Afirka sun yi hasara a fannin cikakken ikonsu na mulkin kai, saboda kasashen yamma sun tilasta musu wasu manufofin tattalin arziki, kana suna yawan alakanta tallafi da zuba jari da batun siyasa. Ban da haka, an gurgunta matsayin daidaito na kasashen Afirka. Alal misali, yayin da manoman kasashen Turai da na kasar Amurka suke samun kudin tallafi mai tsoka daga wajen gwamnatocin kasashensu, ana bukatar manoma da ‘yan kasuwa na kasashen Afirka, su “yi takara cikin gaskiya”, wato ba tare da samun tallafi ba. Wadannan matakai sun haddasa koma bayan masana’antun kasashen Afirka, da sanya su zama masu samar da albarkatun kasa. Haka zalika, rashin samun aikin yi a gida ya sa matasan Afirka kwarara zuwa kasashen waje don neman damar raya kai. A cewar Mista Shikwati, wadannan abubuwan da suka faru sun sa kasashen Afirka daina amincewa da kasashen yamma.
- Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
- Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Wasu manyan kusoshin kasashen Afirka ma sun taba bayyana irin wannan shakku game da tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorantar kasashen yamma. Misali, a kwanan baya shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, ya bayyana a wani taron kungiyar kasashen Turai ta EU cewa, “Muna tattaunawa kan ‘huldar abokantaka’, amma da alama kalmar tana da ma’anoni daban-daban. Ga wasu, tana nufin bayar da umarni da kuma gindaya sharudda, kana a wajen wasu kuma kalmar na nufin bin umarni.” Ya ce tarihi ya nuna cewa irin wannan dangantaka ba za ta haifar da da mai ido ba. Ban da haka, a nasa bangare, Yusuf Tuggar, ministan harkokin wajen kasar Najeriya, yayin da yake ziyarar aiki a kasar Sin a shekarar bara, ya soki tsoma bakin kasashen yamma cikin ayyukan kasashen Afirka ta fuskar harkokin waje, yana mai cewa, “Dukkanmu manya ne, ya kamata kasashen yammacin duniya su daina daukar mu (kasashen Afirka) kamar yara, za mu iya yi wa kanmu zabi.”
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau?
A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai a cikin babbar shawarar inganta jagorancin duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a watan jiya.
Yayin da ake kawo karshen tsohon zamanin da kasashen yammacin duniya ke taka rawa a matsayin masu ba da umarni a duniya, kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka da kasar Sin, za su kara kawo ci gaba mai inganci, da adalci, da daidaito ga duniya, yayin da suke kokarin aiwatar da wasu sabbin tunani, gami da raya su a kai a kai. (Bello Wang)