A yau Litinin 13 ga watan Oktoba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron koli na mata na duniya a birnin Beijing, tare da gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Xi ya jaddada cewa, idan mu yi hangen nesa, za mu ga cewa ya kamata mu waiwayi manufar taron mata na duniya da aka taba yi a Beijing, domin samar da fahimtar juna, da bude hanyoyi masu fadi, da kuma daukar matakai masu inganci don hanzarta ci gaban mata gaba daya.
Game da hakan, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari hudu:
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.
Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu)














