‘Yan bindiga sun sace sace wani ɗan jarida mai aiki da PRNigeria, Salis Manaja, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, domin halartar horon PRNigeria Young Communication Fellowship.
An ce ‘yan bindiga sun sace shi ne a ranar Asabar, yayin da ya taso daga Abakaliki a Jihar Ebonyi zuwa Ilorin.
- Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun tuntuɓi iyalinsa kuma sun nemi kuɗin fansa, sai dai ba a bayyana adadin kuɗin ba.
Shugaban shirin ɗauksr horon, Muhammad Dahiru Lawal, ya ce duk ƙoƙarin da abokan aikinsa suka yi na kiran wayarsa ya ci tura, domin layinsa ya daina shiga bayan an sace shi.
Har yanzu ba a tabbatar da inda aka sace shi ba.
Shirin PRNigeria Young Communication Fellowship dai shiri ne na horarwa da ake gudanarwa kowace shekara a Kano, Abuja, da Ilorin, domin inganta ƙwarewar matasan ‘yan jarida da ma’aikatan kafafen watsa labarai.