Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce rashin tsaro a Nijeriya ba zai ƙare ba sai idan shugabanni sun haɗa samar da ayyukan yi da mulki mai adalci tare da amfani da ƙarfin soja.
Amaechi ya faɗi haka ne a ranar Lahadi, yayin wani taron tattaunawa da matasan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
- Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3
Ya bayyana cewa tushen matsalar tsaro a Nijeriya shi ne talauci da rashin daidaito, ba addini ko ƙabilanci ba.
“Duk wani shugaba da yake son magance matsalar tsaro a Nijeriya dole ne ya gane cewa amfani da ‘yansanda ko soja kaɗai ba zai magance matsalar ba,” in ji Amaechi.
“Ko da an bai wa ‘yansanda da sojoji makamai masu yawa, sauran mutane za su ci gaba da neman makamai domin su mayar wa martani gwamnati.”
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya yi gargaɗin cewa dogaro da soja kaɗai, ba tare da inganta rayuwar jama’a ba, zai ƙara haifar da rikice-rikice.
Ya ƙara da cewa ingantacce tsaro na ƙasa yana farawa ne idan gwamnati ta ƙirƙiro damarmakin samun aiki da kuma mayar da amincin jama’a ga gwamnati.