Rundunar ‘Yansandan Jihar Jigawa ta kama mutane 105 yayin wasu samame da ta kai wa masu fataucin miyagun ƙwayoyi a sassan jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Shi’isu Adam ne, ya bayyana hakan a ranar Talata a hedikwatar ‘yansandan da ke Dutse, babban birnin jihar.
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
- Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa
Ya ce samamen an gudanar da su a wuraren da aka fi samun fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar, inda jami’an ‘yansanda suka yi aiki tuƙuru don daƙile sayarwa da amfani da miyagun ƙwayoyi.
A cewarsa, an kwato sama da ƙwayoyi 5,000 ciki har da tabar wiwi, Tramadol, Exol, D5, da sauran ƙwayoyi masu hatsari.
Ƙwayoyin da aka ƙwato sun haɗa da Exol guda 2,541, D5 guda 1,146, Tramadol fakiti 270, da tabar wiwi sama da 1,000.
‘Yansanda sun kuma samu kuɗi Naira 92,460 da wasu abubuwan maye kamar giya da sauransu.
“Wannan samame sakon gargaɗi ne ga duk masu hannu a fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji SP Adam.
“Yaƙinmu da fataucin miyagun ƙwayoyi yana ci gaba, kuma muna kira ga jama’a su riƙa sanar da mu duk wani abin da suka gani na zargi.”