Yayin da damina ke tin bankwana kuma kaka ke gabatowa a sassan Nijeriya, manoma da dama a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, sun bayyana fargabar rashin girbe amfanin gonarsu saboda hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi yankin.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar suna kai hare-hare kan kauyuka, suna sace dabbobi da kuma garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
- PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai
Wannan ya jefa mazauna yankin cikin halin tsoro da rashin tabbas.
Wani mazaunin yankin ya ce: “Muna cikin wani hali da ba mu taɓa shiga irinsa ba. Amfanin gona ya yi, amma babu wanda zai iya zuwa daji ya girbe. Idan ka je, za su kama ka su kai daji su ce sai an biya kuɗin fansa.”
Ya ƙara da cewa kuɗin da ‘yan bindigar ke nema kan mutum ɗaya sun fi ribar da manomi zai samu idan ya girbe gonarsa.
“Kusan kullum muna cikin tashin hankali a Shinkafi,” in ji shi.
Mutumin ya kuma zargi gwamnati daga matakin tarayya har zuwa ƙaramar hukuma da zuba wa matsalar ido.
“Hare-haren suna ci gaba a Birnin Yero, Jangeru, Shanawa, da Shinkafi kanta. Ko jiya da safe sun kawo hari sun kama manoma.”
A cewarsa, manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron za a sace su. Wasu kuma suna zuwa da dare ne kawai don samun ɗan abin da za su ci.
Sai dai, gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana sane da matsalar da jama’ar yankin ke fuskanta, kuma tana ɗaukar matakai don magance ta.
Mai magana da yawun gwamna, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce: “Gwamnati tana yin duk abin da ya dace domin ta sharewa jama’a hawaye. Yanzu ma an ba jami’an tsaro da shugabannin ƙananan hukumomi umarni su ɗauki matakin gaggawa.”
Ya kuma jaddada cewa gwamnati tana samun nasara a yaƙi da ‘yan bindigar, yana mai cewa ban da yankin Shinkafi, lamarin ya ragu sosai a sauran sassan Zamfara.
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankin suna fatan wannan tabbacin ba zai zama irin alƙawuran da aka saba ji a baya ba waɗanda ba su taɓa kawo canji mai ma’ana ga rayuwarsu ba.














