• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

by Sadiq
1 day ago
Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa, ta ce babu wani ɗan siyasa a Nijeriya da zai iya ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala ne, ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin wani taro da aka gudanar tare da ƙungiyoyi  sama da 100 masu goyon bayan Tinubu.

  • Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu
  • Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Taron mai taken “Tattaunawa da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa,” an shirya shi ne domin bunƙasa haɗin kai tsakanin Fadar Shugaban Ƙasa da magoya bayan Tinubu kafin zaɓen 2027.

Bwala, ya ce manufar taron ita ce a yaba wa ƙungiyoyi da kuma ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da aikin da suke yi.

“Mun zo ne don yi godiya ga ƙungiyoyin da ke goyon bayan shugaban ƙasa bisa irin kokarin da suke yi, tare da roƙonsu su ƙara jajircewa saboda son ƙasa da kuma son Shugaban Ƙasa,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Ya ce manufofi da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata sun ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwa game da tattalin arziƙin ƙasa da tafiyar da gwamnati, abin da ya sa zai yi wuya a kayar da shi a 2027.

“Babu wani ɗan siyasa a yau da zai iya ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Muna tafiya da ‘sabon fata’ zuwa ‘farfafowa,’ kuma wannan farfaɗowar dole ne ta bayyana a rayuwar talakawa,” in ji Bwala.

Ya ƙara da cewa shugabannin ƙungiyoyi daga dukkanin shiyyoyi shida na ƙasar nan sun halarci taron, ciki har da wasu da suka zo daga Biritaniya.

Bwala, ya bayyana cewa taron ba yaƙin neman zaɓe ba ne, amma wata dama ce don gina kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da abokan hulɗa na ƙasa.

“Wasu mutane suna jiran lokacin zaɓe kafin su nemi ƙungiyoyi, amma wannan ba daidai ba ne. Ba kayan aiki ba ne, abokan tafiya ne, dole su kasance cikin abin da gwamnati ke yi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan taruka za a shirya su a Biritaniya, Amurka da Kanada don tattaunawa da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da kuma yaɗa bayanai game da nasarorin gwamnatin Tinubu.

Bwala, ya bayyana cewa Fadar Shugaban Ƙasa tana shirin gudanar da babban taron tattaunawa a watan Nuwamba, inda dukkanin ƙungiyoyi za su haɗu domin nazarin dabarunsu da kuma kimanta yadda gwamnati ke aiki.

Ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ta fara aiwatarwa sun fara bayar da sakamako a fannoni daban-daban kamar makamashi, noma, ayyukan gina ƙasa da samar da ayyukan yi.

“Mun riga mun fara ganin sakamako. Idan muka je fagen aiki, za mu ga ci gaba a bangaren tattalin arziƙi, tsaro, ilimi da noma. Waɗannan ƙungiyoyi za su ci gaba da yaɗa wannan saƙo,” in ji shi.

Shi ma tsohon ɗan majalisa, Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, wanda ya halarci taron, ya yaba wa jagorancin Tinubu.

“Ko mutum ya so ko ya ƙi, Shugaban Ƙasa zai sake lashe zaɓe a 2027. Ba mu kai inda muke so ba tukuna, amma muna cimma nasara. Shugaban Ƙasa na yin duk abin da zai yi don kawo ci gaba,” in ji shi.

Agbonayinma, ya kuma yaba da cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ba da damar a saki maƙudan kuɗaɗe don jihohi su inganta ci gaban al’umma a matakin ƙasa.

Dukkanin masu jawabin sun buƙaci ƙungiyoyin su ci gaba da yaɗa manufofin gwamnati da kuma tabbatar da haɗin kai tsakanin yankuna da jam’iyyu.

Bwala, ya kuma buƙaci magoya bayan Tinubu su ci gaba da nuna goyon baya da ƙauna ga Shugaban Ƙasa.

“Shugaba Tinubu ya yi abin da ya cancanci ba kawai goyon bayan jama’a ba, har ma da soyayya da jajircewarsu don ci gaba da abin da gwamnatinsa ta fara,” in ji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sabbin Ministoci
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Manyan Labarai

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Next Post
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.