A baya bayan nan, Amurka ta gabatar da wasu jerin matakan haraji kan kasar Sin da ma tsarin cinikayya na duniya, lamarin dake mummunar illa ga tsarin ciniki cikin yanci a duniya.
Wani nazari da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar domin jin raayin alummar duniya ya nuna yadda masu bayar da amsa suka yi imanin cewa, Amurka za ta fi yin asara daga yakin cinikin. Sun kuma yi kira ga dukkan kasashe su hada hannu wajen daukar matakan tunkarar irin wadannan matakai.
- Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu
- Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu
Tun bayan tattaunawar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka a watan Satumba, Amurka ta dawo da matsawa Sin ta hanyar kara haraji, ta kuma ci gaba da daukar sabbin matakai domin kuntata mata. Wadannan barazana sun hada da kakaba harajin kaso 100 kan kayayyakin kasar Sin da karin kudin hidimomi a tashoshin ruwa kan jiragen dake da alaka da kasar Sin.
Sakamakon nazarin ya nuna cewa kaso 67.7 na wadanda suka bayar da amsa sun yi ammana cewa, Amurka za ta fi yin asara daga yakin na ciniki, yayin da kaso 8.9 ke ganin kasar Sin ce za ta ji jiki. Kaso 23.4 kuma na ganin illar za ta shafi dukkan bangarorin biyu.
Tun daga farkon bana, Amurka ta yi ta tsananta cin zali ta hanyar kara haraji, inda sama da kaso 70 na kasashe da yankunan duniya suke fuskantar barazanar harajin. Cikin nazarin, kaso 94.4 na masu bayar da amsa sun soki Amurka bisa yadda ta dade tana amfani da tsaron kasa a bangarorin da ba su dace ba domin kare yadda take takaita fitar da kayayyaki ba bisa kaida ba da wariyar da take nunawa kasashe. Sun ce wadannan matakan sun illata muradun sauran kasashe da ma tsarin samar da kayayyaki a duniya.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harshen Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 6572 suka bayar da amsa cikin saoi 24. (Fa’iza Mustapha)













