Alkaluma daga hukumar kula da masana’antar samar da kayayyaki marasa nauyi ta kasar Sin, sun nuna cewa, masana’antar ta samu tagomashi cikin watanni 4 na farkon bana.
Jarin da aka zuba a muhimman bangarorin 6 na masana’antar ya kai maki 2, ciki har da bangaren aikin gona da sarrafa amfanin gona da na sarrafa abinci da fata, wadanda suka samu karuwar sama da kaso 20 cikin dari.
Har ila yau a wannan lokaci, cinikayyar kayayyakin bukatun yau da kullum ita ta yi armashi. Cinikin hatsi ya karo da kaso 9.5 yayin da na mai da kayayyakin abinci da na sha, ya karu da kaso 10.4 a kan na bara.
Hukumar ta kara da cewa, cikin rubu’in farko na bana, cinikin da kamfanonin masana’antar dake samun a kalla Yuan miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 2.97 a shekara suka samu, ya tashi da kaso 9.9 cikin dari zuwa yuan triliyan 5.41.
Bugu da kari, kamfanonin sun samu ribar yuan biliyan 301.02, wanda ya karu da kaso 1.2 cikin dari a kan na bara, lamarin da ya saba da koma bayan da aka saba gani a tsakanin watannin Junairu da Febreru. (Fa’iza Mustapha)