Mutane daga sassa daban-daban da ke garin Lakwaja, ranar Lahadin da ta gabata, suka halarci bikin dattijo mai shekara 74 da ya yi aurensa na farko.
Malam Muhammed Awwal Tanko, mai shekaru 74 a duniya, ya angwance da masoyiyarsa, Malama Jummai Balo, yar shekaru 45.
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
- Jami’an Kashe Gobara Sun Ceto Mutum 91 Da Dukiyar Da Ta Kai Kusan Naira Miliyan 25 A Kano
Bikin daurin auren dai yayi armashi matuka gaya ganin cewa wannan shine karo na farko da Malam Tanko yayi aure a rayuwarsa.
A baya dai sau da dama. sabon angon na Jummai ya yi kokarin neman aure amma lamarin ya faskara duk da cewa yana cikin gatansa. Jama’a sun dai bayyana farin cikinsu da kuma taya ango da amarya murnan wannan rana na aurensu.
Da yake zanta wa da wakilin LEADERSHIP Hausa, Malam Awwal Tanko ya gode wa Allah bisa wannan dama da ya samu a wannan lokaci da yin aurensa na fari.
A karshe, Malam Tanko ya yi kira da babbar murya musamman ga wadanda ba su yi aure ba da su gaggauta yin hakan, domin kamar yadda ya ce, aure wata ni’ima da Allah ya azurta al’umma da ita, kuma ya kamata su ci moriyar wannan ni’imar, musamman wajen samun wanda zai gaji mutum.