Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa raguwar farashin abinci da ake gani a kasuwanni a halin yanzu ya samo asali ne daga ƙaruwar samar da amfanin gona a cikin gida, da fito da kayan da wasu suka boye, da kuma kyakkyawan haɗin gwuiwa tsakanin matakan gwamnatin tarayya da jihohi wajen daidaita isar da kayayyaki.
Ministan harkokin noma da tsaron Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na bikin Ranar Abinci ta Duniya ta shekarar 2025 a Abuja. Ya ce tsare-tsaren noma da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta aiwatar sun fara haifar da gagarumar nasara, inda manoma ke samun ƙarin amfanin gona daga muhimman kayayyakin abinci kamar shinkafa, da gero, da dawa, da rogo, da masara, da wake.
- ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako
- Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Abdullahi ya bayyana cewa rahoton binciken aikin noma na lokacin damina na 2025 da cibiyar NAERLS ta gudanar ya tabbatar da samun ci gaba a fannin noma. Ya ce hakan sakamakon ƙarin jarin da gwamnati ke zuba wa ne ta hanyar tallafin kayan noma, da rancen kudi, da shirin injinan noman zamani wanda ya rage wahalar manoma kuma ya ƙara yawan amfanin gona da ake samu.
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta bayan da fifiko ga tsaron abinci, ba kawai wajen samarwa ba har ma wajen tabbatar da cewa talakawa na iya saya. Abdullahi ya ce yanke shawarar gwamnati na neman shigo da ɗan ƙaramin adadin abinci a bara ya sa masu boye kaya suka saki nasu saboda tsoron asara, wanda hakan ya ƙara yawan kayayyaki a kasuwa kuma ya sa dole a rage farashi.
A cewarsa, gwamnatocin jihohi suma suna taka rawa wajen kafa manyan rumfunan ajiya don daidaita farashi, musamman a jihohin Kaduna, da Kano, da Jigawa da Neja. Ya ce gwamnatin tarayya tana ci gaba da tallafawa manoma ta hanyar bayar da kayan noma kyauta da sauƙaƙa musu samun injinan noma domin rage kuɗin samarwa da ƙarfafa ci gaba da noman zamani.