Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, yana fuskantar rashin tabbas a kan burinsa na takarar shugaban kasa a shekarar 2027, yayin da ake ta samun rudani a jam’iyyar da yake kokarin tsayawa takara.
Rahotannin sun bayyana cewa Obi, wanda ya yi takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam’iyyar LP, yana daga cikin manyan mambobin jam’iyyar hadaka ta ADC da ke shirin kawar da Shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
A ranar 2 ga Yulin 2025, shugabannin ‘yan adawa da suka hada da Obi, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark, tsofaffin gwamnonin Jihar Kaduna da Ribas, Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi, sun zabi ADC a matsayin jam’iyyar da za su goyi baya a zaben 2027.
Ko da yake, fatan Obi na samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a ADC yana fuskantar matsala, yayin da manyan ‘yan jam’iyya ke nuna muradi ga Atiku.
Wata majiya daga jam’iyya ta shaida cewa ba za a sami dan takara a jam’iyyar ba har sai ta gudanar da zaben fid da gwani kamar yadda sauran jam’iyyun siyasa suke yi, ADC za ta gudanar da zaben fitar da gwani don tantance wanda zai yi wa jam’iyyar takara.
Saboda haka, an samu labari daga bangaren Obi cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa ba za yi zaben fid da gwani ba da Atiku.
Sai dai kuma, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ki cewa uffan kan jita-jitan da ke cewa jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zaben fid da gwani, wanda hakan ya saba wa tsammanin wasu mambobin, musamman daga bangaren Obi.
A cewar Bolaji, a halin yanzu ADC ba ta mai da hankali kan wane zai tsaya takara a karkashin tutan jam’iyyar ADC a zaben 2027 ba.
“A halin yanzu dai, babu wanda aka tattaunawa kan cewa shi ne sahihin dan takara ko kuma za su gudanar da zaben fitar da gwani. Idan mun kai ga wannan lokaci, za mu yi bayani.
“Wannan ba shi ne abin da muke fifita a wannan lokaci ba. Har yanzu mu jam’iyya ce sabuwa kuma muna mai da hankali kan yadda za mu bunkasa jam’iyyarmu a yanzu. Wannan ya fi muhimmanci a gare mu fiye da magana kan ‘yan takarar shugaban kasa”, in ji shi.
Game da dalilin da ya sa Obi bai yi rajista a matsayin mamba na jam’iyyar ba, Bolaji ya ce, “Mun ce Obi da El-Rufai ba su da katin mamba na ADC tukuna saboda yana son goyon bayan ‘yan takarar jam’iyyarsa ta siyasa ta asali a zaben da ke tafe.”
“A game da Peter Obi, bayan zaben Jihar Anambra ne zai iya zaman cikakken dan jam’iyyar ADC. Idan kuma akwai wani dalili, to ban sani ba.”
A gefe guda kuma, wasu masana siyasa sun yi ikirarin cewa da yiwuwar Obi ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 a karkashin jam’iyyar LP wacce take da saukin rikici a cikinta.
Wani masanin siyasa, Dakta Anabi Samuel, ya shaida cewa burin tsayawa takarar shugaban kasa na Obi ba zai samu nasara a jam’iyyar LP ba, sakamakon rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar.
A cewar Anabi, rarrabuwan kai da aka samu saboda shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure da wadanda ke cikin tawagarsa za su kawo cikas ga Obi.
“Peter Obi ya samu makiya da yawan gaske a LP, don haka za iyi wuya ya samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
“Kamar jagoran reshen jam’iyyar, Julius Abure, zai tabbatar cewa ya kawo masa cikas tun daga zaben fid da gwani kuma zai yi wuya su ba shi tikiti kai tsaye.
“Mu kaddara ma ya sami tikitin LP, sai ya fuskanci makiya daga wajen jam’iyyar wadanda za su tabbatar da cewa bai yi nasara ba.
“Idan Obi ba zai iya samun tikitin ADC ba, ya kamata ya dakatar da burinsa na takara, sai dai idan PDP ta amince za ta ba shi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa.
“Akwai jita-jitan da ke cewa yana shirin shiga sabon jam’iyyar siyasa. Ya kamata Obi ya watsar da wannan tunanin. 2027 ba kamar 2023 ba ce, yana bukatar jam’iyya da aka sani da kyakkyawan tsari don samun nasara a zaben 2027”, in ji Anabi.
Ko da yake wasu masu nazarin harkokin siyasa suna ganin cewa Peter Obi ne ya haskaka jam’iyyar LP, sai dai kuma jam’iyyar ta nace cewa tsohon gwamnan ba zai samu tikitin kai tsaye ba a 2027.
Sakataren yada labaran na wani bangare na LP, Obiora Ifoh ya shaida cewa bai dace ba a ba Obi tikitin kai tsaye.
“Za a gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyarmu. Za a wallafa mukaman da ake da su kuma duk wanda ke da sha’awa zai nema ya bi tsarin zaben fid da gwani yadda ya kamata.
“Ba tsarin dimokuradiyya ba ce na bai wa wani dan takara tikiti kai tsaye,” in ji Ifoh.