Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa ya amince da karin kashi 100 na alawus- alawus da ake ba dalibai a rukunoni daban- daban na manyan makarantun da suke Jihar.
Gwaman idan ba a manta ba a watan Yuli 2025, lokacin da yake ganawa da manema labarai yayi kokarin karin kudin tallafin da ake ba wa dalibai da kuma biyansu cikin lokaci.
- Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka
- Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi
Ma’aikatar ilimi mai zurfi ta Jihar ta ce dalilin matakin kamar yadda Gwamnan ya nuna shi ne yadda yake da bukata ta yin jagoranci nigari, da kuma niyyarsa ta sai Jihar Gombe ta kas a gaba a lamarin daya shafi bunkasa d aci gaban ilimi.
A wani jawabin da aka yada ta kafar sadarwar zamani ta shafin Facebook jiya, ma’aikatar ta kara da cewa tun lokacin da shi Gwamnan ya dare kan Kujerar mulkin Jihar, mulkin gwamna Inuwa ya kafa dokar ta baci kan lamarin daya shafi ilimi, inda ya bullo da tsare tsare da zuba jari da zummar bunkasa bangaren ilimiin.
Wadanda za su amfana da karin tallafin kudin karatun sun hada dalibai masu karatun da suka hada da PhD, MSc, PGD, BSc, HND, NCE, ND, da kuma Satifiket.
Da yake na shi jawabin wajen sa albarkacin baki kan ci gaban da aka samu, Shugaban kungiyar dalibai ‘yan asalin Jihar da suke Jami’ar Jihar Gombe, Abubakar Muhammad Yamanga, ya bayyanawa LEADERSHIP cewa alawus din da dalibai suke amsa yanzu Naira 7,500, ko dayake dais au da yawa su kan amshi Naira 7,000 bayan wasu cire- ciren da aka yi.
“Wannan ya nuna da yake an riga an bayyana karin, da aka yi, ana kuma sa ran dalibai za su rika amsar fiye da Naira 14, 000. Tuni dai aka riga aka biya Naira 21,000 kowane inda aka biya wasu kudaden da, ba a biya ba can baya,” in ji shi
Kamar dai yadda ma’aikatar ilimi mai zurfi ta bayyana, gwamnan ya amince da karin da aka yiwa mutane masu bukata ta musamman, jim kadan bayan da aka kirkiro hukumar kulawa da lamurran masu bukata ta musamman ta Jihar.
Hukumar bada tallafin karatu ta Jihar Gombe ta bada sanarwar lamarin tantancewa da za ayi domin a samu gano dukkan daliban da suka cancanta su amfana, za a fara cancancewar nan bada dadewa ba da kuma ranakun da za ayi haka, da kuma duk yadda za ayi ita tantancewar.