Tawaga ta 28 ta likitocin kasar Sin mai aikin tallafin jinya a kasar Togo, ta gudanar da ayyukan duba marasa lafiya, da bayar da magunguna kyauta ga yara marasa galihu, a wani kauye dake kusa da birnin Lome, fadar mulkin kasar.
Yayin aikin jinyar da tawagar ta gudanar a jiya Asabar, likitocin sun duba lafiyar yara kanana 32, dake zaune a wani gidan marayu mai lakabin “Ray of Hope” na kauyen Yope Kope, mai nisan kilomita kusan 60 daga arewa maso yammacin birnin Lome. Likitocin sun yiwa yaran gwajin lafiyar jiki, da ido da dai sauransu.
Wannan aiki dai wani bangare ne na shirin “Goyon bayan juna ta fuskar kiwon lafiya tsakanin Sin da Togo na shekarar nan ta 2025”, wanda aka kaddamar a watan Maris, karkashin jigon “Aiki tare domin samar da kyakkyawar makoma ga yara.”
Da take jawabi dangane da aikin na wannan karo, shugabar tawagar ta 28, ta likitocin kasar Sin dake Togo Guo Juanjuan, ta ce sun dukufa wajen yaukaka kawance da al’ummun nahiyar Afirka, ta hanyar samar da kwarewar aiki, bisa abota da tausayawa, da wanzar da burin marasa lafiya na samun waraka. (Saminu Alhassan)














