Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ‘yan wasanta Ogenyi Evans da kuma babban kociyan kungiyar, Ahmed Garba (Yaro-yaro) nan take, biyo bayan abin da mahukuntan kungiyar suka bayyana da rashin gamsuwa da irin matakin kungiyar a gasar firimiyar Nijeriya ta 2025/2026 da ke gudana.
A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da sadarwa na kungiyar, Abubakar Isah Dandago ya sanya wa hannu, hukumar ta ce, “an dakatar da mai horas da ‘yan wasa Ogenyi Evans da kuma babban kociyan kungiyar, Ahmed Garba (Yaro-yaro) nan take, sakamakon rashin gamsuwa da kokarin kungiyar a kakar wasan 2025/2026 na gasar firimiyar Nijeriya”.
- Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong
- Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu
Sanarwar ta kara da cewa, rashin samun kyakkyawan sakamako ne ya sanya mahukuntan kungiyar yanke wannan hukuncin, bayan da ta buga wasanni 8 kawo yanzu da nasara 2 kacal, ta yi canjaras 2, da kuma rashin nasara 4.
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha.