Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce ba a yi wa Kiristoci wani kisan gilla a Arewacin Nijeriya, inda ya bayyana irin waɗannan zarge-zarge a matsayin ƙarya da nufin raba kan al’umma.
Sarkin ya bayyana haka ne a taron Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.
- Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
- Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba
Ya ce, “Tun fil azal Kiristoci da Musulmai suna rayuwa tare cikin zaman lafiya a Arewa. Waɗannan zarge-zarge ba gaskiya ba ne, kuma manufarsu ita ce tayar da rikici tsakanin ‘yan uwa.”
Sarkin ya yaba wa rundunar sojin Nijeriya bisa jajircewarsu wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Arewa da kuma sassan ƙasar baki ɗaya.
Ya kuma tabbatar da goyon bayan sarakunan gargajiya ga Gwamnatin Tarayya da dakarunta wajen ci gaba da yaƙar rashin tsaro.
“Da ba sojoji, da ba za mu iya gudanar da wannan taro cikin kwanciyar hankali ba. Don haka dole mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwa,” in ji shi.
Sarkin Musulmi ya kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo ba tare da tunani ba, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace don tsara amfani da su, inda ya bayyana cewa shi kansa ya taɓa fuskantar matsala bayan yaɗa labaran ƙarya a kansa.