Wani bincike da Jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa, ayyukan da ke gudanarwa a Tashar Jiragen Ruwa ta Kantudu da ke a jihar Kaduna sun ja baya matuƙa
A cewar binciken, hakan ya faru ne, saboda dakatar da gudanar da ayyukan zirga-zirgar Jiragen Ƙasa da ke tasowa daga Tashoshin Jiragen Ruwa na jihar Legas saboda ƙalubalen rashin tsaro da kuma yadda ambaliyar ruwan sama, ya lalata wani sashe na Titin Jirgin ƙasa.
- Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin
- Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa
A shekarar 2018 Marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne, ya ƙaddamar da Tashar.
An tsara ta ne, domin sauke kayan da Jiragen Ruwa suka yo jiglarsu tare da kuma tura kayan a cikin sauƙi, zuwa ga guraren da aka tsara kaisu da kuma rage cunkoso a Tashar Jiragen Ruwa ta jihar Legas, wanda hakan kuma zai taimaka masu motocin da za su yi safafar kayan .
Sai dai, bisa wasu bayanai da Jaridar LEADERSHIP ta samu sun bayyana cewa, Jiragen Ruwan sun gaza yin jigilar kaya daga Tashar Jiragen Ruwa ta jihar Legas shekaru da dama da suka gabata zuwa Tashar ta kantudu da ke a jihar Kaduna, musamman saboda yawan aukuwar ayyukan ‘yan bindiga a jihar Neja da kuma yadda ambaliyar ruwan sama ta lalata wasu sansan hanyar layin Dogo da ke yankin Mokwa
Waɗannan matsalolin, sun sanya ake yin jigilar kayan ta kan hanya, a manyan motoci, wanda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin ke ci gaba da kokawa, saboda kuɗaɗen da suke kashewa masu yawa, wajen jigilar kayansu
wanda hakan ya saɓawa manufar ta kafa Tashodhin Jiragen Ruwan ta kantudu.
Injiniya Kayode Opeifa Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa na ƙasa ya tabbatar da waɗannan matsalolin a taron 2025 Ƙungiyar ‘Yan Jarida Wakilai da ke ɗauko rahotannin ɓangaren sufuri TCAN, da aka gudanar a jihar Legas.
A cewar Kayode, ƙalubalen rashin tsaro, a jihar Neja, hakan ya tilasta Hukumar dakatar da jigilar kayan ta hanyar amfani da Jirgin ƙasa zuwa Kaduna.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Neja da Kaduna, sun yi haɗaka domin lalubo da mafita kan lamarin.
Wani Babban Jami’i a Tashar ta kantudu da ke a jihar Kaduna wanda bai buƙaci a sakaya sunansa ya shedawa LEADERSHIP cewa, baya ga ƙalubalen rashin tsaro, ambaliyar ruwan sama da ta auku a jihar Nije, ta janyo yin gaba da wasu ƙarafan da Jirgin ƙasa ke bi, wanda hakan ya dates ɗaukacin duk wata zirga-zirgar Jiragen zuwa Tashar.
“Muna ci ga da jiran Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta ƙasa NRC, domin ta gyran hanyar ta layin Dogon, wanda kuma idan harkar tsaro ta ƙaru, hakan zai bai wa masu hada-hadar safarar kaya a Jiragen Ƙasan, su samu damar ci gaba da yi zuwa Tashar ta Kantudu, da ke a jihar ta Kaduna, “ A cewar babban jami’i.
Ya ƙara da cewa, yayin da ayyukan sufurin suka tsaya tska, hakan ya sanya ba a yin safarar kaya a cikin Jiragen zuwa Tashar.
Sai dai, wasu masu ruwa da tsaki a fannin sun bayyana fargabar da cewa, ci gaba da ɓata lokaci da ake yi na rashin yin amfani da Tashar hakan zai karya masu ƙwaiwa na ci gaba da yin amfani da Tashar wajen yin safarar kayansu zuwa Tashar.
Bugu da ƙari, sun bayyana cewa, hakan zai kuma mayar da hannun Agogo bayan na ƙiƙarin Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ɗaga darajar Tashoshin na Kandu, da aka samar a ƙasar, musamman wajen samar da sauƙin gudanar da hada-hadar kasuwanci a yankin Afirka.
Sai dai, duk da wannan ƙalubalen Hukumar ta NRC da kuma sauran gwamnonin jihohin da abin ya shafa, na kan yin aiki daomin sake dawo da zirga-ziragar kaya zuwa Tashar ta hanyar ƙara ƙarfafa tasaro da kuma sanya wasu ƙarafan na layin Dogo, da ambaliar ruwan saman, ta yi gaba da su.














