Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojojin rundunar hadin gwiwa, Operation Hadin (OPHK) Kai, sun dakile wani hari a Gamboru Ngala, inda suka kashe ‘yan ta’adda 10 tare da kwato makamai.
Kakakin rundunar hadin gwiwa ta yaki da ‘yan ta’adda, Kanar Sani Uba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ya kara da cewa, bata kashin ya faru ne a yankin Gamboru-Dikwa-Marte.
Nasarar, ta biyo baya-bayan irin nasarar da aka samu kwanan nan inda sojojin suka kashe ‘yan ta’adda sama da 50 a Katarko, jihar Yobe, in ji shi.
Kanar Uba ya ce, ‘yan ta’adda sun kutso cikin garin ne ta yankin Flatari sannan suka tsere da raunuka zuwa Dikwa “bayan sun sha ruwan wuta.”














