Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa.
Lamido ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya kuma bayyana shirin ziyartar sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja don samun fom din takararsa.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno
- Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
“Da yardar Allah, a yau, Litinin 27 ga Oktoba 2025, da karfe 11 na safe, zan kasance a Wadata Plaza, hedikwatar jam’iyyarmu ta kasa, PDP, don sayen fom din tsayawa takara don neman mukamin Shugaban Jam’iyyar na kasa,”in ji sanarwar.
Tsohon gwamnan, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar PDP kuma fitaccen mai fada a ji a cikin jam’iyyar, yana neman jagorantar jam’iyyar yayin da take shirin yin babban taronta na kasa.
Ana sa ran jam’iyyar PDP, wacce ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2015, za ta zabi sabon Shugabanta na kasa da sauran shugabannin jam’iyyar a lokacin babban taron jam’iyyar da za a yi a Ibadan a jihar Oyo a watan gobe.














