Shugaban Kamfanin rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, ba za a samu karancin man fetur a kasar ba a watannin bukukuwan Kirismati da karshen shekara ba kamar yadda aka saba samu duk shekara a fadin Nijeriya.
Da yake magana a ranar Lahadin davta gabata yayin da yake sanar da fadada Matatar Man Fetur ta Dangote daga ganga 650,000 a kowace rana (bpd) zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana, attajirin ya ce, masana’antar ta shirya tsaf don biyan buƙatun gida ba tare da wani ƙarin farashi ba, duk da hauhawar farashin man fetur na duniya a ‘yan kwanankin nan.
“A cikin kwanaki uku da suka gabata, an samu hauhawar farashi da kashi 8 cikin 100 na farashin man fetur a duniya,” in ji Dangote. “Amma ina so in tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, Matatar Dangote ta kuduri aniyar ci gaba da samar da man fetur ba tare da katsewa ba a duk lokacin bukukuwan Kirismati da karshen shekara. A karon farko cikin shekaru da yawa, ‘yan Nijeriya za su iya fatan Kirsimeti da Sabuwar Shekara ba tare da fargabar man fetur ba.”
Wannan tabbacin ya zo ne a daidai lokacin da farashin famfon mai ke canzawa a faɗin ƙasar, wanda tun daga kusan ₦189 a kowace lita a shekarar 2023 zuwa sama da ₦1,000, kafin ya daidaita tsakanin ₦800 da ₦900 a farkon shekarar 2025.














